China ta hana yara amfani da intanet da daddare
Yan yaran ba za su yi amgani da wayar ba tsawon dare
Hukumar kula da amfani da shafukan intanet ta kasar China ta kafa wata sabuwar doka da za ta takaita tsawon lokacin da yara ke shafewa suna amfani da wayoyinsu a intanet.
Matakin dai zai kawo babban cikas ga kamfanoni irin su Tencent da ByteDance, wadanda su ne manyan masu shafukan intanet da wasannin da ake yi a intanet a kasar.
- ‘Barayi’ sun kone shaguna 20 bayan yin sata a tsohuwar kasuwar Gombe
- Kanawa ne suka bukaci a cire sunan Maryam Shetty daga minista ba ni ba – Ganduje
A ranar Laraba ce dai hukumar ta wallafa kundin sabuwar dokar a shafinta na intanet, inda ta ce a yanzu, ba za a kyale kananan yara su yi amfani da intanet da daddare ba.
Kazalika, ta ce yara masu shekara 16 zuwa 18 a yanzu za su rika amfani da intanet ne kawai na tsawon awa biyu kacal.
Bugu da kari, yara masu shekara 8 zuwa 15 za su rika amfani da intanet na awa daya kacal, ’yan kasa da shekara 8 kuwa za su iya shafe minti 40 ne kawai a kullum.
Dokar ta ce wasu shafuka da kawai aka yi ittifakin suna da amfani ga yara za a kyale su su yi amfani da su sama da wannan lokacin. Sai dai hukumar ba ta yi bayani a kan shafukan ba.
Wannan sabon matakin dai shi ne irinsa na baya bayan nan da gwamnatin China take sanyawa domin rage yawan sabon da yara ke yi da intanet, matsalar da ta ce ta tasam ma zama ruwan dare.
Ko a shekara ta 2019, sai da gwamnatin ta rage tsawon lokacin da yara za su iya shafewa suna wasanni ta intanet zuwa minti 90.
A shekara ta 2021 kuwa, an dada tsaurara matakan inda aka mayar da awa dayan kawai a ranakun Juma’a da Asabar da Lahadi da kuma ranakun hutu.