China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas
ByteDance zai nemi aƙalla dala biliyan 40 zuwa 50 wajen sayar da manhajar ta TikTok.
Rahotanni na cewa Gwamnatin China ta soma shirye-shiryen sayar da manhajar sadarwar nan ta TikTok ga fitaccen attajirin duniya, Elon Musk.
A ranar Litinin da ta gabata ce Jaridar Bloomberg ta ruwaito cewa manyan jami’an China sun soma muhawara dangane da tsare-tsaren amfani da TikTok a matsayin wani ɓangare na gudanar da muhimmiyar tattauna game da aiki tare da gwamnatin Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka, Donald Trump.
- Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 — NBS
- Mutum 14 sun rasu sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa a Taraba
Bayanai sun ce China ta soma duba yiwuwar sayar da TikTok reshen Amurka ga Mista Musk ne domin kare manhajar daga yawan dakatar da ayyukanta da ake yi a ƙasar.
Sai dai wasu majiyoyi da ke da masaniya game da batun sun ce manyan jami’an China sun fi so manhajar ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin ikon kamfanin ByteDance Ltd.
A makon jiya ne, Kotun Ƙolin Amurka ta bayyana cewa za ta amince da dokar dakatar da ayyukan TikTok a Amurka a ranar 19 ga watan Janairun nan – kwana ɗaya kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Donald Trump – saboda matsalolin tsaron ƙasa da ke da alaƙa da China.
A ɓangare guda rahoton na Bloomberg ya ce shafin X na Elon Musk — wanda a baya aka fi sani da Twitter — zai karɓi ragamar ayyukan TikTok a Amurka kana zai ci gaba da gudanar da dukkan kasuwancinsa
Haka kuma, rahoton ya ce zuwa yanzu jami’an ba su kai ga cimma ƙwaƙƙwarar matsaya ba kan wannan tsari.
“Babu tabbaci ko ByteDance na da masaniya game da tattaunawar gwamnatin China ko kuma yiwuwar sanya TikTok da Musk cikin batun.
“Kazalika, babu tabbacin cewa Musk da TikTok da kuma ByteDance sun tattauna game da sharuɗɗan yiwuwar yarjejeniyar,” in ji rahoton.
Tuni dai masana harkokin kasuwanci da Bloomberg ta tuntuɓa sun bayyana cewa matuƙar ciniki ya faɗa, ByteDance zai nemi aƙalla dala biliyan 40 zuwa 50 wajen sayar da manhajar ta TikTok a reshen da ke Amurka.
A wani rubutu da mai yi wa jaridar Wedbush fashin baƙi kan harkokin kasuwanci, Dan Ives ya wallafa a ranar Talata, ya ce farashin manhajar ta TikTok zai iya kai wa wannan darajar la’akari da da farashin dala biliyan 44 da Mista Musk ya saye manhajar Twitter a 2022.