China za ta yi dokar takaita yada addini a kafofin sadarwar zamani
Gwamnatin kasar China ta fara shirye-shiryen yin wata doka da za ta takaita yadda ake yada lamuran addini a kafofin sadarwar zamani, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito daga jaridar Global Times. A sabuwar dokar, dole duk wanda yake son ya ci gaba da yada addininsa ya nuna sha’awar haka ga gwamnati, […]
Gwamnatin kasar China ta fara shirye-shiryen yin wata doka da za ta takaita yadda ake yada lamuran addini a kafofin sadarwar zamani, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito daga jaridar Global Times.
A sabuwar dokar, dole duk wanda yake son ya ci gaba da yada addininsa ya nuna sha’awar haka ga gwamnati, sannan gwamnati ta ba shi lasisin da zai ba shi damar ci gaba da yada addininsa, amma kuma za a ci gaba da lura da ayyyukansa.
Kuma duk da cewa za a ba shi lasisin, sabuwar doka za ta takaita ne kawai a kan yada lamuran addini da koyarwa, amma ba za a amince a rika yada lamuran addini kai-tsaye ba. Sannan kuma za a saka ayyukan ne a shafin Intanet da aka bude domin hakan, don haka ba za a amince da sanyawa a wata manhajar ba.
Haka kuma dokar za ta sanya kafar wando daya da wadanda suke yada kalaman batanci, musamman masu adawa da tsarin gwamnatin kasar,da kuma masu zafin ra’ayin addini.
A ka’ida, duk dan kasar China yana da damar yin addininsa matukar addinin yana cikin addinan da aka sani a kasar. Amma gwamnatin ta dade tana yaki da masu yada addini ba tare da lasisi ba, musamman Musulmi da masu bin addinin Kirista na bangaren Protestant.
An dade ana sukan yadda gwamnatin kasar ke danne hakkin Musulmi a kasar, musamman Musulmin yankin Uighur a Arewa maso Gabashin dinjiang.