Chuchu: Kotu ta hana a gwada ƙwaƙwalar matar da ta kashe yaron gidanta

Idan wanda ake ƙara ya yi mata magana tana amsawa, amma idan kotu ta yi mata magana sai ta yi shiru.

Chuchu: Kotu ta hana a gwada ƙwaƙwalar matar da ta kashe yaron gidanta

Kotu

Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta ƙi amincewa da buƙatar da lauyoyin Hafsat Sani Suraj suka gabatar na neman kotun ta ba da umarnin kai wadda suke karewa asibiti domin a gwada ƙwaƙwalarta.

Ana iya tunawa, wacce ake ƙara Hafsat Suraj — da aka fi sani da Hafsat Chuchu —mazauniyar Unguwa Uku a Jihar Kano tana fuskantar tuhumar kisan wani yaron gidanta mai suna Nafiu Hafizu, wanda idan ya tabbata hukuncinsa kisa ne ƙarƙashin sashe na 221 na Pinal Kod.

Lauyan Gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Halima Yahuza Ahmad ta shaida wa kotun cewa a ranar 21 ga watan Disamba, 2023, Hafsat Suraj ta yi amfani da wuƙa ta caccaka wa marigayin a ƙirjinsa da wasu sassa na jikinsa, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Haka kuma, ana zargin mijin Hafsat Suraj wato Dayyabu Abdullahi da laifin taimaka mata wajen aikata laifi, sai dai lokacin da aka karanta masa takardar tuhumarsa ya musanta laifin da ake zarginsa da shi.

Sai dai lokacin da aka karanta mata laifin da ake tuhumarta da shi ta yi shiru, lamarin da lauyoyinta ƙarƙashin jagorancin Barista Sani Ammani suka nemi kotun ta bayar da umarnin kai ta Asibitin don gwada ƙwaƙwalarta.

Lauyar Gwamnatin Halima Yahuza ta yi suka game da bukatar tasu.

Da yake yanke hukunci, Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Faruk Lawan ya bayyana cewa kotun ba ta ga wani abu na rashin hankali a tare da wacce ake ƙara wanda har zai sa a kai ta asibitin a gwada ƙwaƙwalarta ba.

Alƙalin ya ƙara da cewa don haka za a ɗauke ta a matsayin wacce ta musanta zargin da ake yi mata.

“Na lura cewa idan wanda ake ƙara na biyu ya yi mata magana tana amsawa, amma idan kotu ta yi mata magana sai ta yi shiru.”

Haka kuma ya ɗage zaman shari’ar zuwa ranar 13 da 14 da 15 ga Agusta, 2024 domin sauraron shaidu.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa