Ci gaba daga makalar da aka sanya ranar Juma’a 23 ga watan Janairu

Shi dai Alhaji Bala, tun lokacin da Ladidi ta buda bakinta, har izuwa yanzu bai samu amsar da zai ba ta ba. Sai dai kawai ya ci gaba da kallonta tamkar an dauke wuta a cikin magudanar jinin jikinsa. Can dai sai ya yi ta maza ya tambaye ta sahihancin binciken da ya nuna cewa […]

Ci gaba daga makalar da aka sanya ranar Juma’a 23 ga watan Janairu
Ci gaba daga makalar da aka sanya ranar Juma’a 23 ga watan Janairu

Shi dai Alhaji Bala, tun lokacin da Ladidi ta buda bakinta, har izuwa yanzu bai samu amsar da zai ba ta ba. Sai dai kawai ya ci gaba da kallonta tamkar an dauke wuta a cikin magudanar jinin jikinsa. Can dai sai ya yi ta maza ya tambaye ta sahihancin binciken da ya nuna cewa ’yarsu na dauke da juna biyu. Ita kuma ta tabbatar masa babu wani kokwanto a cikin sakamakon. Har ma dai idan akwai kokwanto shi ne; Shin fyade aka yi wa Zuwaira ne, ko kuma tsoratar da ita aka yi ta bayar da kai bori ya hau? Domin tabbas bincike bai nuna wata alama da ke nuna an taba saduwa da ita da karfin tsiya ba. Kuma duk wanda ya san Zuwaira, ba zai taba tsammanin cewa za ta aikata wani abu mai kama da hakan ba.

Abin da ya haifar da wannan rudun, hatta mutanen unguwa, babu wanda ya san zuwaira na sauraren maza. Dare da rana karatu ne a gabanta da kuma al’amuran da za su amfane ta. Baya ga hankali da sanin ya kamata, kowa na shaidarta da tsabar jin tsoron Allah, domin kuwa tun tana yarinya karama ba ta son a yi zalumci, kuma ba ta yarda da abin da zai zubar da kimarta. kare da karau ma, idan kina son zama lafiya da ita, to ba za ki taba kawo mata tsegumin kowa ba. Domin ba ta zagin mutane kuma ba ta yarda a ci mutuncinsu ba.
‘’Zuwaira, ni ce mahaifiyarki, kuma na yarda da ke dari bisa dari! Da ni da mahaifinki babu abin da kika nema gunmu kika rasa, kuma mun tarbiyantar da ke gwargwadon ikonmu, har sai da kika kasance abar alfahari da bayar da misali a cikin kawayenki. Ya aka yi hakan ta faru a gare ki? Ina hada ki da Allah ki buda baki ki yi magana.’’ Ladidi ce ta fadi hakan a lokacin da ta kurawa Zuwaira ido.
‘’Tabbas dukan abin da nake nema a gurinku ba wanda nake rasawa, kuma kun ba ni tarbiya yadda ya kamata, amma kun kasa biya min bukatar da ta rinjaye ni kuma wadda ita ce sanadiyar wannna hali da nake a ciki.. Kuma har abada ba zan yafe muku ba’’ Zuwaira ce ta furta hakan a cikin daukaka murya ba tare da tsoro ko fargaba ba’’ Ta kuma saki jikinta tsaf kamar ba abin da ke faruwa, kuma ba kamar yadda ta shigo dakin ba. Sai ta ci gaba da bayaninta da cewa:‘’Mahaifiyata bai dace ace kin manta da maganar da kika taba fada min ba,cewa TSORON ALLAH SHI KAdAI BA ZAI HANA YIN SAbO BA HAR SAI AN NISANCI
ABIN DA ZAI SA A YI SAbON, wanda har kika ce wannan ne dalilin da ya sa ake son mutum ya yi hijira daga garin da sabon Allah ya yawaita zuwa inda ake yi wa Allah biyayya.’’ Ko na gaya muku cewa babu sha’awar aure a tare da ni bai dace ku gasganta ni ba, amma a haka kuka bar ni dare da rana ina cudanya da ’ya’ya maza! Ni mutum ce tamkar kowa, ina da sha’awa kuma shaidan yana bibiyata, me ne ne abin mamaki idan har…..’’
Tun kafin Zuwaira ta kare wannan bayani nata, nadama ta bayyana a idanun mahaifanta, suka tabbatar da cewa lalle sun makara, kuma kibiyar tsautsayi ta riga ta soke su. Kuma suka fahimci cewa idan ana gudun sabon Allah,wajibi ne a nisanci wuraren sabon. Domin haka tarbiyantar da yarinya kadai
ba ya wadatarwa har sai an nisantar da ita daga wuraren da akan iya sauya mata wannan tarbiya.
Mun kammala.
Za a iya samun Nasir a 08033186727