Ci gaban mai hakar rijiya aka samu a Arewa – Mu’azu Alhaji

Wani dan uwa ga Marigayi Sardauna, Alhaji Mu’azu Alhaji, ya bayyana cewa marigayi Sardauna Ahmadu Bello mutum ne mai son taimaka wa na baya. Ya ce, Sardauna tare da wadansu amintattunsa sun yi hangen nesa inda suka gina bankin Arewa (Bank of The North) da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da Filin wasa Ahmadu […]

Ci gaban mai hakar rijiya aka samu a Arewa – Mu’azu Alhaji
Ci gaban mai hakar rijiya aka samu a Arewa – Mu’azu Alhaji

Wani dan uwa ga Marigayi Sardauna, Alhaji Mu’azu Alhaji, ya bayyana cewa marigayi Sardauna Ahmadu Bello mutum ne mai son taimaka wa na baya.
Ya ce, Sardauna tare da wadansu amintattunsa sun yi hangen nesa inda suka gina bankin Arewa (Bank of The North) da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da Filin wasa Ahmadu Bello a Kaduna da Otel din Hamdala da Gidan rediyon Kaduna (BCNN)  da Kamfanin raya Arewa (NNDC)  da kamfanin buga Jaridun ‘New Nigerian’ da Gaskiya Ta Fi Kwabo da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Polytechnic) da Masaku a Kakuri, Kaduna da gadar da ta ratsa kogin Kaduna da Asibiticin koyarwa a Zariya da Kaduna da kuma Malumfashi da dai sauransu. Amma yanzu wadansu ko fenti an kasa yi musu fiye da shekaru goma, sannan wasu sun zama tarihi, domin an ruguza su.
Alhaji Mu’azu Alhaji, wanda da ga marigayi Sarkin Shanu Alhaji Alhaji, ya ce idan har akwai sauye-sauyen da aka samu tun bayan rasuwar Sardauna, sune inda gidan Sardauna ya zama  ‘Gidan Arewa,’ aka cire wayan daya kewaye gidan aka yi katanga aka zagaye shi aka mai da shi otel. Kuma an sauya gidajen Ministoci zuwa mashaya da kuma dandalin sheke aya, inda ake sayar da giya. Gidan shawara na sarakunan Arewa (Lugard Hall) kuma aka mayar da shi Majalisar dokoki ta jihar Kaduna. Sannan katafaren shagon Kingsway ya koma ginin banki da ofishin Hukumar kiyaye hadurra da wadansu ofisihi. Sannan ginin kamfanin New Nigerian ya zama kango, don ai daina buga jaridun. Ginin kamfanin NNDC yana nan ba wani sauyin kirki. Sannan katafarun shaguna Bhojsons da Lebentis da kuma Chalaram da sauransu sun zama tarihi.
 Alhaji Mu’azui Alhaji ya kara da cewa, ginin ofishin Magajin Gari na Kaduna da Filin Wasa na Ahmadu Bello da gadar da ta ratsa kogin Kaduna suna nan babu garanbawul. Jerin gidajen manyan sakatarori da ke gefen filin sukuwa a Kaduna a yanzu an gina gidaje da shaguna a tsakaninsu, wanda hakan ya bata tsarinsu. Kuma an sare bishiyoyin da aka tarar a wurin. Wani abin takaici kuma  shine yadda aka rugurguza masakun da Sardauna ya gina. A yanzu Kaduna, watau cibiyar Arewa ta zama kusan kango, don an keta mata haddi. Atakaice muna iya cewa mun samu ci gaba irin na mai hakar rijiya. Alhaji Mu’azu Alhaji ya kara da cewa, sai dai a ce Sardauna ya yi hakuri, don an ci amanarsa, an lalata abubuwan da ya kafa ba tare an maida madadinsu ba. Yace mafita ita ce a kalli gaba.