Ci-rani ya zama matsala a Taraba

Sanarwar da gwamnatin jihar Taraba ta bayar  a ranar 21 ga watan Janairu na wannan shekarar  inda ta bayyana dakatar da wadasu hakimai da dakatai bakwai, ta jawo ka ce – na ce a sassa daban-daban na kasan nan.Sanarwar  dai ta fadi dalilin da ya sa gwamnan jihar Darius Ishaku ya dakatar da masu sarautun […]

Ci-rani ya zama matsala a Taraba

Sanarwar da gwamnatin jihar Taraba ta bayar  a ranar 21 ga watan Janairu na wannan shekarar  inda ta bayyana dakatar da wadasu hakimai da dakatai bakwai, ta jawo ka ce – na ce a sassa daban-daban na kasan nan.
Sanarwar  dai ta fadi dalilin da ya sa gwamnan jihar Darius Ishaku ya dakatar da masu sarautun gargajiyan su bakwai. A cewar sanarwar, an dakatar da masu sarautun gargajiyan ne saboda sun bai wa wadansu baki ‘yan ci-rani da suka fito daga wadansu jihohin arewancin kasar nan filaye lokacin da suka yi gudun hijira saboda rigingimun kabilanci da makamantansu.
Wancan sanarwar wadda babban Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Hassan Mijinyawa ya sanya wa hannu, ta  zargi hakiman da bai wa baki  wadanda suka fito daga jihohin  Zamfara da Kano da Jigawa da Yobe da Sakkwato da kuma Neja filaye. A cewa sanarwar, wadannan mutane sun kasance barazana ga zaman lafiyar jihar. Kuma ana zarginsu da laifin aikata miyagun laifuka, kamar  fashi da sauran muyagun laifuka.
Bincike ya nuna cewa   tsohon gwamnan jihar Taraba danbaba Suntai ne ya fara sanya jami’an tsaro su binciki  baki ’yan ci-rane da suka fito daga jihohin arewancin kasar nan.  kuma lokuta da dama ana nuna cewa wadannan bakin  ba su da wani muhimmin dalili na zuwa jihar ta Taraba. Tun daga wancan  lokaci ne aka fara wulakanta ’yan ci-rani a jihar Taraba, saboda ana yi musu kallon cewa sune suke aikata laifuka a jihar.
Wadannan mutane yawancinsu sukan shigo jihar ta Taraba ne don neman kudi, musamman a lokutan kaka watau bayan an ci amfanin gona. Kamar yadda bincike ya nuna ’yan ci-ranin kan shigo jihar ta Taraba ne tare da iyalansu su zauna na kusan watanni uku zuwa hudu, watau daga watan Disamba zuwa watan Afrailu.
Irin ayyukan da ‘yan ci-ranin ke gudanarwa a lokacin zamansu a jihar sun hada da noman rani da  kamun kifi da sayar da ruwa da da sayar da itace da sayar da Rake da yankan farce da wanzanci da sayar kayan miya, da dai sauran sana’o’i daban-daban.
Jami’an tsaro a lokuta da dama sun tasa keyar daruruwan ’yan ci-rani zuwa wajen jihar,  domin a wadansu makwabtan jihar, kamar Filato da  Binuwai da  kudancin Jihar Borno da wadansu daga cikin jihohin yammacin da kudancin kasar nan  an kyale su ba tare da nuna masu wata tsangwama ba.
Ana dai kallon wannan lamarin da shi tsohon gwamnan ya bullo da shi da cewa wariya ce ta fuskar addini da kabilanci. Wannan lamarin ya yi kamari ne a farkon wannan shekarar a lokacin da wani Sanata wanda ke wakilta kudancin jihar Taraba a Majalisar Dattijai  mai suna Sanata Emmanuel Bwacha ya ce wai ‘yan Boko Haram suna kwarara zuwa jihar ta Taraba. Jin wannan ikirari da shi Sanatan ya yi, sai jami’an tsaro suka  soma gudanar da bincike ga duk wanda zai shigo jihar.
Hanyoyi da jami’an tsaro suka dauka, kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar Alhaji Sha’aba Alkali ya fada, ita ce ta bincike ’yan ci-rani masu shigowa jihar daga makwabtan jihar, wato daga jihohin Gombe da Yobe da Borno da  Bauchi da Jigawa, da dai sauran jihohin arewancin kasar nan, don gano masu laifi.
Kwamishinan ya baiyana cewa a iyakacin bincikensu ba su samu wata shaida da ta nuna cewa ‘yan ci-ranin da suke shigowa jihar ‘yan Boko Haram ne ba.
Alhaji Alkali ya bayyana cewa, a binciken da suka gudanar sun tasa keyar wadansu zuwa inda suka fito, domin sun kasa bayar da takamammiyar dalilinsu na zuwa jihar ta Taraba.
Kwamishinan ya kara da cewa,  jami’ansa sun samu wata mota dauke da mutane maza da mata da yara har su 50, amma bincike ya nuna wadannan mutane mafi yawa daga cikinsu sun gudo ne daga jihohin Borno da Yobe da Adamawa saboda rigingimun da ke faruwa a can. Wadansu cikinsu suna da ‘yan uwa a nan jihar Taraba.
Alhaji Bala Hamza, dan asalin jihar ta Taraba ne, ya shaida wa wakilinmu cewa, duk lokacin da ka ji an fidda da irin wannan sanarwa za ka iske ana neman a aiwatar da wani shiri ne wanda zai haifar da rashin zaman lafiya.
Ya kara da cewa, “a yankin Wukari akwai ‘yan kabilun Yarkam daga jihar Filato, wadanda ya yi zargin cewa suna tare da sojojin sa-kai na kabilar Jukunawa, wato Jukun’Youth militia.’ Kuma su ne ake zargi da kashe daruruwa musulmai  tare da satan dubban shanu a yammacin jihar, wato yankin Wukari, amma saboda kasancewarsu ’yan lele gwamnati ta ki cewa komai a kansu.’’
Ya ci gaba da cewa, “a gariuruwan Wukari da Ibbi an samu fadace-fadace fiye da sau goma 13 kuma rigirgimun suna da alaka da kabilanci da addini, wanda ya haifar da asarar rayuka sama da dubu, tare da barnata dukiyoyi na miliyoyi Naira, amma babu wani mataki da aka dauka na hukunta masu hannu a wadannan fadace –fadacen.’’
Sai wadda ta auku tsakanin  kabilun Shomo da Jule a karamar hukumar Lau. ‘Yan kabilar Shomo ne ake zargi da tayar da fitinar, inda suka fada wa ‘yan kabilar Jule, suka kashe jama’a da yawa, har da wadanda ba su ji ba su gani ba. Laifi ‘yan kabilar Jule shi ne, sun bai wa ’yan ci-rani  wadanda aka kira kabawa aron wurin noman rani.
Shi ma da yake magana kan wanana lamari, wani mai suna Mista Jacob Dauda, ya bayyana cewa, bai kamata a ware ‘yan wadansu jihohin kasar nan a ce haramtatun baki ba ne, har ma a danganta su da aikata laifuka.
Ya ce duk dan Najeriya na da ‘yancin zama a duk wani sashi na kasar nan, muddin zai kasance mai bin doka da kuma daraja aladun jama’ar wurin da yake zaune.
Ya kara da cewa, akwai hanyoyin da dokar kasar nan ta tanadar na hukunta duk wanda ya aikata laifi, amma ba a kore mutum a wani bangare na kasar nan ba, don kawai shi ba dan wancan bangaren ne ba.
Sai dai kuma Kwamishin watsa labarai na jihar ta Taraba Lauya Anthony Danburam ya bayyana wa Aminiya cewa an ari bakin gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku aka masa albasa da shi, domin kuwa a cewarsa, gwamnantin jihar Taraba tana maraba da baki daga duk inda suka fito, musamnan ma “’yan Arewa, muddun dai za su shigu jihar da niyya mai kyau. “Mu ‘yan Arewa ne kuma ‘yan Arewa ‘yan uwanmu ne, ba za mu hana kowa shiga Jiharmu don neman abinci ba,” inji Kwamishinan watsa labarai.
Ya ci gaba da cewa, mutane ba su fahimci abin da wannan sanarwa take nufi ba ne, gwamna bai ce wa wadansu ’yan wata jiha masu aikata laifa ba, a’a a nan yana nufin cewa ba daidai ba ne a ba wadansu mutane filaye  wadanda suka yi gudun hijira, kamar yadda masu sarautun da aka dakatar suka yi.
Lauya danburan ya kara da cewa, dokar kasa ta bai wa ’yan kasa damar zama a duk inda suke so, amma fa dole ne su kasance masubin doka da daraja al’adun jama’ar inda suke zaune.
Ya kara da cewa, ’yan ci-rani akwai abubuwan da za su koya wa jama’ar jihar ta fuskar ayyukan neman kudi, kamar su noman rani da sauran sa’o’i, wanda ta haka ne kawai jama’ar jihar za su daina zaman kashe wando.