Ci-rani ya zama matsala ga ’yan Arewa

kungiyar kare muradun  Arewa (ACF) da kungiyar Jama’atu da wadansu fitattun mutane sun yi Allah wadai da kama wadansu ‘yan Arewa mutum dari hudu da tamanin da shida da sojoji suka yi a jahar Abiya da sunan wai  su ‘yan Boko Haram ne.kungiyar Jama’atu ta nuna rashin jin dadinta da kama mutanen da suka fita […]

Ci-rani ya zama matsala ga ’yan Arewa
Ci-rani ya zama matsala ga ’yan Arewa

 ’YanArewa 486 da aka kama a Jihar Abiya lokacin da suke kan hanyar zuwa Fatakwal ci-rani a bisa zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne.kungiyar kare muradun  Arewa (ACF) da kungiyar Jama’atu da wadansu fitattun mutane sun yi Allah wadai da kama wadansu ‘yan Arewa mutum dari hudu da tamanin da shida da sojoji suka yi a jahar Abiya da sunan wai  su ‘yan Boko Haram ne.
kungiyar Jama’atu ta nuna rashin jin dadinta da kama mutanen da suka fita domin neman halaliyarsu alhali babu wani makami da aka samu a tare da su.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Kaduna dangiwa Umar ya nuna cewa hakan da aka yi yana iya jawo tunzuri a kasa.
ACF ta kuma bukaci gwamnonin Arewa sha tara da su gaggauta tattaunawa da sauran takwarorinsu na kudu akan wannan batu domin a sako mutanen da aka kama ba tare da bata lokaci ba.
Da yake tattaunawa da Aminiya ta wayar tarho, shugabzn kungiyar ACF kuma Sardaunan Katsina, Alhaji Ibrahim Kumasi, ya ce gaskiya abin da sojoji suka yi ya bata musu rai, domin bai kamata su kama mutanen da ba su da makami a nuna su a ce ‘yan ta’adda ne.
“ Wannan abu dake faruwa ba daidai ba ne, kuma ai na fada a cikin jawabina a lokacin da na hau wannan mukami, kuma mun fada wa gwamnoninmu na Arewa cewa su yi magana da takwarorinsu na kudu da su daina irin wannandomin  ba daidai bane. Saboda bayanai sun nuna mana cewa ba a samu komai ba da ya nuna cewa su ‘yan Boko Haram ne, domin babu bindiga ko wani makami da ke nuna cewa su ‘yan ta’adda ne, sai kawai a kama su babu gaira babu dalili, bayan an matsa musu a garuruwansu sun fito neman abinci kuma sai a kama su.’’
“Ba mu yarda ba ko kadan, kuma ba mu ji dadin abin da ya faru ba. Matakin da za mu dauka shi ne za a tattauna a ofishinmu a kan abin da za mu yi, domin a yanzu ina halartar taron hadin kan kasa, kamar yadda ka sani, amma za a dauki mataki,” inji shi.
Game da jan hankalin jami’an tsaro kuwa, sai ya ce, “ ai kullum muna jan hankali cewa biI kamata a rika ji wa ‘yan kasa ba kuma ga shi kasa na cikin wani hadari, sannan a  ce kuma an cigaba da musguna wa mutane  babu gaira babu dalili, ai bai dace ba.’’
“Duk matakan da za mu dauka za a dauka domin magance irin wannan matsala. Ina matukar yin Allah wadai da wannan abu da ya faru, sannan ina  yin kira ga gwamnonin Arewa da su yi magana da sauran gwamnonin kudu a kan aikata irin wannan abu, musamman kama mutanenmu ‘yan Arewa da ake yi, Gaskiya su daina,” inji shi.
A ranar Litinin ne dai sojoji suka kama mutum 486 a Jihar Abiya, wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Fatakwal.
Bataliyar sojoji ta 144 da ke Asa kusa da garin Aba suka kama wadannan mutanen. Sojojin sun ce sun kama mutanen ne da misalin karfe 2 na dare tsakanin sha-tale-talen Arungwu da kuma kofar Imo Gate da ke kan iyakar Jihar Abiya da ta Ribas. Sun ce wadannan mutane sun yi jerin gwano ne a cikin motocin bas-bas 36.
Har lokacin rubuta wannan rahoton, sojojin suna ci gaba da tsare wadannan mutane don gudanar da bincike don tabbatar da zamansu ’yan Boko Haram ko akasin haka.
Mutanen sun fito daga jihohin arewacin Najeriya ne da suka hada da Bauchi da Jigawa da sauransu, an kama su ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa  garin Fatakwal. Jama’a da dama sun ce al’amarin cike yake da nuna wariya da kuma tsangwama ga ’yan arewacin Najeriya.
Sai dai ana cikin wannan cece-kucen ne sai Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya ta yi ikrarin cewa ta gano wani babban dan ta’adda da take nema ruwa a jallo a cikinsu.
A cikin watan Janairun wannan shekarar ma sojoji sun kama wadansu matafiya da suka fito daga areawacin kasar nan su 300 a Jihar Ribas, amma da manyan Arewa suka tashi tsaye sai aka sako su.
Tashar BBC Hausa ta rawaito daya daga direbobin wadannan motoci mai suna Murtala Muhammad Kasala-Babu yana cewa wannan wani shiri ne na musguna wa ’yan Arewa.
Ya ce: “Babu batun jerin gwano, tafiya ce muke yi ta rana daya, wani ya tashi karfe daya, wani sha biyu, wani karfe daya, wani tun karfe shida na safe ma zai tashi. Idan haka ne tafiyar ba za ta zama daya ba, idan ma an hadu bai wuce motoci uku ko hudu ba, wani ma shi kadai yake tafiyarsa. Ina so mutane su gane yadda kabilun Kudu suke zuwa Arewa, mutanen Arewa ba sa zuwa Kudu haka. Su ba a yi musu komai ba, sai mu da muke zuwa Fatakwal? Motocin Macpolo daya, sai ta dauki adadin motoci da yawa da muke dauka, idan a ce za a kama duk motar da ta shigo Kano daga Kudu, Ibo nawa za a kama? Dubu nawa za a kama?”
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa kama mutanen da aka yi yana iya yuwuwa wata makarkashiya ce aka shirya domin ‘yan Arewa su daina shiga motocin haya na ‘yan uwansu ‘yan Arewa domin zuwa gabashin kasar nan.
Aminiya ta gano cewa, sojojin sun kama wani shugaban al’umma da ya je domin jin dalilin kama wadannan mutanen.
Bala Mato Dambam, wanda shi ne Shugaban kungiyar ’Yan Tireda na Arewacin Najeriya da ke Yankin Malife da ke Fatakwal, ya ce  wannan kamun da aka yi, yana nuna kabilanci da nuna wariya da tsangwama da kuma tsana ga ’yan Arewa a Kudu.
Dokta Usman Zinnurain, wanda malami ne a Tsangayar Nazarin Shari’a a Jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana cewa, a shari’ance da kuma tanadin da kundin tsarin mulki ya yi, kowane dan kasa yana da ’yancin ya je ko’ina a kasar nan, “Don ya gudanar da harkokinsa ba tare da tsangwama ba. Idan wani yanayin ya faru da aka kama mutum, sannan ake zarginsa da aikata wani laifi, hakkinsa ne a shari’ance a fada masa laifin da ake zarginsa da aikatawa da kuma dalilin da ya sa aka kama shi, sannan a ba shi cikakkiyar dama ta kare kansa.”
Ya ce, “Idan an kama wani, sai wani nasa ya je don ya ji dalilin kama shi, sannan shi ma aka kama shi, to wannan ba daidai ba ne, don haka wannan ba zai hana mahukuntan jihohin da wadannan mutanen suka fito, kamar Jihar Jigawa daukar mataki ba.”
Wakilinmu ya tuntubi Charles Ajinwa, Daraktan yada labarai na gwamnan Jihar Abiya, wanda ya je barikin sojan da ake tsare da wadannan  mutanen, inda ya ce, “Sojoji sun kama mutane dari hudu da tamanin da shida, wadanda ake zargi masu tayar da kayar baya ne a Jihar Abiya, yanzu haka ana yi musu tambayoyi, hukumomin soja za su sanar da jama’a abin da suka gano game da mutanen”.
Da Aminiya ta tuntubi Mato Dambam, shugaban kungiyar ’yan Arewa masu sana’ar tireda da ke Mil Uku a garin Fatakwal, ya karyata zargin da ake yi  wa mutanen, “Wadannan mutane masu gudanar da kananan sana’o’i,  tun daga tura kura zuwa yankan farce, zuwa sayar da karas da rake, ba masu tayar da kayar baya ba ne, kuma sun saba zuwa kowace shekara cin rani a nan garin Fatakwal,” inji shi.
Shugaban ya bayyana cewa, sama da shekara goma mutanen nan suna zuwa neman kudi a Jihar Ribas, yanzu haka dai, a cewarsa, sun sanya manya a gaba domin karbo mutanen daga hannun jami’an na soja tun da dai duk abin da ake zato za a samu na laifi gare su ba a samu ba.
Da yake karin haske, Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki na Jihar Jigawa, Alhaji Abdu Dauda ’Yankwashi, ya ce wadanda aka kama din ba ’yan asalin Jihar Jigawa ba ne kawai, amma suna nan suna shirin tashin wakilai daga jihar domin ganin sun kwato mutanen daga wajen sojojin.
Ya nuna damuwarsa game da irin yadda ake kama mutanen jihar a yankunan Abiya da Ribas, inda yake ganin  akwai bambancin siyasa da kabilanci a cikin lamarin. Ya kara da cewa, lamarin yana sa jama’ar Jigawa cikin barazana, musamman wadanda suke tafiya yawon ci-rani.
Hedikwatar Rundunar Tsaron Najeriya dai ta fitar da sanarwa mai dauke da cewa a cikin binciken da ake gudanarwa ga wadanda aka kama din, ta gano wani kasurgumin dan ta’adda da sunansa ke cikin jerin sunayen ’yan ta’addar da take nema ruwa a jallo, sai dai sanarwar ba ta bayyana sunansa ko karin bayani kan dan ta’addan ba.