CIA da Mossad ne ke taimakon Boko Haram da ISIL – Shugaban Sudan
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al-Bashir ya ce Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA) da takwararta ta kasar Isra’ila MOSSAD suna da hannu a ayyukan kungiyoyin ’yan ta’adda da suka hada da Boko Haram d ISIS. Omar al-Bashir ya bayyana haka ne a tattauawarsa da kafar labarai ta Euronews inda ya yi da’awar cewa akwai […]
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al-Bashir ya ce Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA) da takwararta ta kasar Isra’ila MOSSAD suna da hannu a ayyukan kungiyoyin ’yan ta’adda da suka hada da Boko Haram d ISIS.
Omar al-Bashir ya bayyana haka ne a tattauawarsa da kafar labarai ta Euronews inda ya yi da’awar cewa akwai alaka a tsakanin hukumomin leken asiri na Amurka da Isra’ila da kungiyoyin biyu.
Ya bayyana haka ne bayan kungiyar ISIS ta sako wani faifan bidiyo da ke nuna ana sarekan wasu Kiristoci 21 na darkar Coptic a kasar Libiya, lamarin da ya fusata Masar ta mayar da martani da kai farmaki da jiragen yaki don daukar fansar kisan gillar.
Al-Bashir ya shaida wa kafar labaran cewa: “Na ce CIA da Mossad suna tallafa wa wadannan kungiyoyi; babu Musulmin da zai iya gudanar da irin wancan aiki.”
Boko Haram ta sace ’yan mata kusan 300 daga makarantar sakandaren Chibok a bara, kma a bayan nan ta dauki alhakin kisan kare-dangi a garin Baga, inda a faifan bidiyon da ta fitar ta yi gargadin cewa wannan “somin tabi ne.”
Su ma mayakan ISIS sun kashe dubban jama’a a hare-harensu na zubar da jini a kasashen Syriya da Iraki.
Al-Bashir ya yi gargadi kan daukar matakin zubar da jini da sunan yaki da masu daukar makamin, inda ya ce hakan yana iya kara haifar da mugun martani daga masu tsaurin ra’ayin.
Ya ce “Tsarinmu yana matukar samun nasara, bayan mun kama irin wadannan matasa muka hada su da matasan malamai su tattauna da su kan fahimtarsu, kuma mun samu nasarorin dawo da su kan fahimta ta kwarai daga tsattsaurar fahimtarsu.”
Bayanin nasa ya zo ne bayan Shugaban kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ya ce CIA da MOSSAD na da hannu a ayyukan kungiyoyi masu tsarin ra’ayi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito.