Cibiya ta horar da manoman lambu 100 a Gombe

Cibiyar Nazari Kayan Marmari da na Lambu ta Kasa (National Horticultural Research Institute- NHRI), ta zakulo manoma 100 daga Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe inda ta koyar da su dabarun noma da sarrafa takin gargajiya ta hanyar mayar da shara zuwa taki. A jawabin Babban Bako kuma Shugaban Ofishin Cibiyar da ke Bagauda […]

Cibiya ta horar da manoman lambu 100 a Gombe

Ana miqa wa waxansu daga cikin mahalarta horarwar irin gwaiba

Cibiyar Nazari Kayan Marmari da na Lambu ta Kasa (National Horticultural Research Institute- NHRI), ta zakulo manoma 100 daga Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe inda ta koyar da su dabarun noma da sarrafa takin gargajiya ta hanyar mayar da shara zuwa taki.

A jawabin Babban Bako kuma Shugaban Ofishin Cibiyar da ke Bagauda a Jihar Kano, Alhaji Idris Bala Giginyu, ya ce suna horar da manoman ne musamman matasa domin su kware a vangaren noma da sanin dabarun sarrafa takin gargajiya domin rage dogaro da takin zamani.

Alhaji Idris Bala Giginyu, ya ce suna koya wa mata a gida yadda za su yi karamin lambu a gida, domin karamin wajen a cikin gidajensu da nufin rage wahalhalun yau da kullum ta hanyar ci da kuma sayarwa.

Ya ce suna tattara sharar da ke gona ta karan masara da na dawa da sauran nau’o’in shara irin su vawon lemo ta hanyar tona rami a binne a zuba ruwa har tsawon wata uku idan suka ruve su zama taki.

Shugaban Ofishin Cibiyar da ke garin Dadin-Kowa a Jihar Gombe, Alhaji Mu’azu Ya’u Gwammaja, ya ce dukkan wadanda suka halarci wannan horo za su amfana.

Ya ce suna koya wa manoman yadda za a sarrafa takin gargajiya ne saboda ya fi rashin illa ga lafiyar mutane a kan takin zamani, kuma zai dade yana aiki a gona ba kamar takin zamani da zai kare a shekara daya ba.

Wadansu daga cikin wadanda suka amfana da shirin da suka yi magana a madadin sauran, Muhammad D. Ibrahim da Hajara Shu’aibu, sun yaba wa cibiyar bisa wannan horo da suka samu inda suka ce ya kara musu ilimi matuka.

A karshen horon na wuni daya an raba wa mahalarta taron irin mangwaro da gwaiba, don su je su ci gaba da rainonsu su girma, inda za su amfana da su zuwa wani lokaci a gaba.