Cibiyar Al’adu ta Birtaniya ta horar da ’yan jarida dabarun aiki a  Adamawa

Cibiyar Ala’adu ta Birtaniya (British Council) da hadin gwiwar Kungiyar Dakile Fadace-Fadace a Arewa maso Gabas, (MCN) sun horar da manema labarai dabarun aiki bisa yadda za su tsara labarai a lokutan rikici ta yadda ba za su tada hankulan jama’a ba. Taron na kwana biyu, wanda aka gudanar Yola fadar Jihar Adamawa an shirya […]

Cibiyar Al’adu ta Birtaniya ta horar da ’yan jarida dabarun aiki a  Adamawa

Waxansu daga cikin waxanda ake zargi da kisan Janar Alkali da suka samu beli a Jos

Cibiyar Ala’adu ta Birtaniya (British Council) da hadin gwiwar Kungiyar Dakile Fadace-Fadace a Arewa maso Gabas, (MCN) sun horar da manema labarai dabarun aiki bisa yadda za su tsara labarai a lokutan rikici ta yadda ba za su tada hankulan jama’a ba.

Taron na kwana biyu, wanda aka gudanar Yola fadar Jihar Adamawa an shirya shi ne don rage matsalolin barkewar rikici a Arewa maso Gabas musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Shugaban MCN a Jihar Adamawa, Abdulkadir Bello Ahmed ya bayyana cewa sun shirya taron ne domin karin ilimi ga manema labarai wajen rubutawa ko watsa labarai, yadda za a kauce wa ta da hankulan jama’a a lokutan zabe ko kuma barkewar rikice-rikice a yankunan.

Mista Bonat Tagwai daya  daga cikin wadanda suka gabatar jawabi kan illolin yada labaran kage a tsakanin al’umma, ya bayyana labaran kagen a matsayin abubuwan da suke  haddasa rudani a tsakanin al’umma. Bonat ya gargadi manema labarai su daina yada labaran kage wadanda za su haddasa rudani a tsakanin al’umma musamman a wannan lokacin da zaben shekarar 2019 ya gabato.

Wata malama a taron, Hajiya Laurat Abdulsalam ta ce manema labarai su kasance masu gaskiya wajen gudanar da ayyukansu domin samar wa kawunansu suna mai kyau da kuma inganci.

Shugaban Ma’aikata na Jihar Adamawa, Dokta Edger Amos ya ce wannan taron da aka shirya ya zo a daidai lokacin da aka fi bukatarsa, domin nan ba da dadewa ba za a fara gudanar da zaben 2019, sannan ya bukaci manema labarai su yi adalci a yayin gudanar da ayyukansu.