Cibiyar Alfurkan da kungiyar Almasdar sun shirya wa malamai bita

Aminiya: Da farko muna so ka gabatar mana da kanka? Bismillahir Rahmanir Rahim. Da farko sunana Ali Rabi’u Ali. Na san ga duk wadanda su ka dade suna kallon fina-finai sunana ba bako ba ne a wajensu. Nine shugaban kamfanin A.R.A Mobies da ke kano wacce kamfani ce da ke harkar fadakarwa ta hanyar shirya […]

Cibiyar Alfurkan da kungiyar Almasdar sun shirya wa malamai bita

Aminiya: Da farko muna so ka gabatar mana da kanka?

Bismillahir Rahmanir Rahim. Da farko sunana Ali Rabi’u Ali. Na san ga duk wadanda su ka dade suna kallon fina-finai sunana ba bako ba ne a wajensu. Nine shugaban kamfanin A.R.A Mobies da ke kano wacce kamfani ce da ke harkar fadakarwa ta hanyar shirya fina-finai masu ilmantarwa da nishadantarwa tare da nuna al’adu da kuma addini domin fadakar da mutane.

Aminiya: Kwanakin baya akwai wasu shirye-shirye da wata cibiya da ke da mazauni a garin Kano mai suna Alfurkan ta gudanar wanda kana daya daga cikin wadanda suka tafiyar da wannan aiki, a matsayinka na daya  daga cikin masu ruwa da tsaki, ko za ka kara mana haske a kan irin wannan shirye-shiryen?

Na ji dadin yin wannan tambayar da ka yi. Hakika shi wannan shiri da Alfurkan tayi abu ne mai matukar fa’ida da kuma amfani domin shiri ne da zan iya bugan kirji in ce ba a saba yin irin sa a wannan yanki namu ba domin na farko su Alfurkan za mu iya cewa sun fahimci irin cutar da ke damun al’ummarmu sai kuma suka nemo maganin da ya dace da wannan ciwon suka barbaba a kai. 

Akwai kalubalen da kafafen watsa labarai ke fuskanta musamman kafofin addinin musulunci don haka ne wannan cibiya ta shigo tare da sanyawa wannan cutar maganin da ya dace tare da nuna musu yadda za su rika aiwatar da al’amuran.

Aminiya: Ko za ka bayyanawa al’umma irin yadda shirye-shiryen su ke?

Wato shiri ne wanda aka tsara shi ta yadda akan zo da malamai na addinin musulunci masu wayewa ta yadda in sun zo a cikin shirin a kan yi musu tambayoyi kan abubuwan da ya shafi addinin musulunci su kuma suna bada amsa haka. Tambayoyi ne dai kan batutuwa da dama da suka shafi zamantakewa da tarbiyyar al’umma da kuma hukunce-hukunce na ibada da sauransu.

Aminiya: Kasantuwar yadda al’ummarmu su kayi nisa wajen kallon fina-finai na nishadantarwa kana ganin irin wadannan shirye-shiryen za su yi tasiri a cikin mutane?

kwarai kuwa! Domin ai kowane irin shiri za ayi akwai hikimomin da a kan yi amfani dasu domin jawo hankalin masu kallo ko masu sauraro. Kowane abu ya kan samu karbuwa ne bisa ga irin salon da aka bi da kuma irin mutanen da suka gudanar. Misali shi wannan aiki ka ga wata kamfani ce daga kasar Sudan wacce ake kira Almasdar ta gudanar dashi wacce ita cibiyar Alfurkan din ta gayyato su musamman don su yi musu wannan shirin wanda sun yi haka ne don a samu aiki mai kyau na zamani tare da kayan aiki na zamani wanda zai bada sauti da hoto mai kyau kuma alhamdu lillahi mun ga kwarewar Almasdar din da irin kwararrun ma’aikatansu kuma an kammala cikin nasara. Kamar yadda na ce ma ka su Almasdar suna dukkan harkokin da suka shafi aikin gidajen talabijin, fara wa da assasa gidajen Talabijin da kuma bube sutudiyo tare da bayar da horo ga duk wanda yake son bude gidan talabijin ko son gabatar da wasu shirye-shirye haka to su kan bayar da shawarwari a kai. Don haka a karshe ina kira ga sauran kungiyoyi na addinin musulunci da su yi koyi da cibiyar Alfurkan wajen gudanar da irin wadannan shirye-shiryen don taimakawa addinin musulunci.