Cibiyar bincike na kokarin alkinta irin jakuna a Najeriya

Cibiyar Bincike Kan Dabbobi ta Kasa Dake Zariya (NAPRI) da hadin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kansu na kokarin kafa wuraren kiwo a jihohin Bauchi da Ebonyi domin alkinta jinsin jakunana a Najeriya. Babban daraktan cibiyar, Farfesa Abdullahi Mohammed shine ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Zariya ranar […]

Cibiyar bincike na kokarin alkinta irin jakuna a Najeriya

Jakuna

Cibiyar Bincike Kan Dabbobi ta Kasa Dake Zariya (NAPRI) da hadin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kansu na kokarin kafa wuraren kiwo a jihohin Bauchi da Ebonyi domin alkinta jinsin jakunana a Najeriya.

Babban daraktan cibiyar, Farfesa Abdullahi Mohammed shine ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Zariya ranar Lahadi.

Ya ce tuni cibiyar tasu ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninsu da wani kamfani mai suna Earthwheel Logistics da ma wasu a watan Fabrairu domin samar da jakuna akalla miliyan biyu nan da shekaru biyar zuwa goma masu zuwa.

A cewarsa, ana sa ran samarwa da kasar kudaden shiga akalla Dala biliyan biyu ta hanyar jakunan, wanda hakan ya zo daidai da manufar gwamnatin tarayya ta fadada hanyoyin samun kudaden shiga musamman ta harkokin noma da kiwo.

Ya ce, “A sakamakon hakan, mun lura cewa jinsin jakuna na cikin barazanar karewa a Najeriya. Hakan ne yasa Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Kasa ta ayyana su a matsayin dabbobin da suke cikin hatsarin karewa saboda safararsu da ake yi daga arewa zuwa kudu ana ci.

“Kazalika, mun lura cewa ana yin magungunan gargajiya da su musamman a kasashen nahiyar Asiya,” inji shi.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta yi wani hobbasa wajen ganin ta magance matsalar.

Ya kuma ce tuni cibiyar ta su ta kafa sama da wuraren adana su inda yanzu haka take da sama da jakuna 100 a ajiye.