Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa

Cibiyar ta ce wasu daga cikin cin zarafin mata da ake yi al’ada ba addinin Musulunci ba.

Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa

Cibiyar Bunƙasa Ayyukan Bincike za ta gudanar da gangami domin nazarin dokokin da suka shafi zamantakewar Musulmi a jihohin da ta ke aiki, domin inganta haƙƙoƙin mata da ƙananan yara.

Shugaban tawagar cibiyar, Dokts Taofik Abubakar daga Jami’ar Bayero Kano ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da suka kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya.

Dokta Taofik, ya ce sun je fadar ne, domin neman albarka da shawarwari kan hanyoyin magance cin zarafin mata.

Ya kuma bayyana cewa cibiyar ta ɗauki nauyin malamai da limamai zuwa Jami’ar Al-Azhar da ke Masar don ƙaro ilimi kan matsayin Musulunci game da cin zarafin mata.

A cewarsa, cin zarafin mata al’ada ce da aka gada daga tsohuwar ɗabi’a, ba addinin Musulunci ba.

Ya ƙaryata fahimtar da wasu ke da ita cewa Musulunci yana goyon bayan miji ya doki matarsa, inda ya jaddada cewa Annabi Muhammad (SAW), ya haramta hakan.

Cibiyar za ta gudanar da gangamin tattaunawa da shugabannin jihohin Kano da Kaduna domin nazarin dokokin da suka shafi zamantakewar Musulmi, tare da ƙoƙarin tabbatar da su matsayin doka.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya buƙaci a sake nazarin dokar zamantakewar Musulmi da aka yi watsi da ita a Kano, domin inganta haƙƙoƙin mata a Arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa haƙƙoƙin mata ba su da ƙarfi a tsarin dokokin shari’a na yankin, wanda ke haifar da cikas ga rayuwarsu.

Ya ce idan aka tabbatar da dokar, zai taimaka wajen kare haƙƙin mata da yara a Arewa.

Sarkin ya kuma buƙaci da a gaggauta tabbatar da dokar a jihohin da ake gudanar da aikin, domin ta zama doka da za a bi a duk faɗin Najeriya.