Cibiyar Bunkasa Al’umma ta Alhuffaazh za ta kafa jami’a a Lere

Daraktan Cibiyar Bunkasa Al’umma ta Alhuffaazh da ke garin Saminaka a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Dokta Muhyideen Ibrahim Salahudden ya ce cibiyar za ta kafa jami’a  a yankin.  Dokta Muyideen Ibrahim Salahudeen ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin bikin bayar da kyaututtuka da neman gudunmawa don ginin […]

Cibiyar Bunkasa Al’umma ta Alhuffaazh za ta kafa jami’a a Lere

Dokta Muhyiddeen Ibrahim SalahuddeenDaraktan Cibiyar Bunkasa Al’umma ta Alhuffaazh da ke garin Saminaka a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Dokta Muhyideen Ibrahim Salahudden ya ce cibiyar za ta kafa jami’a  a yankin.  
Dokta Muyideen Ibrahim Salahudeen ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin bikin bayar da kyaututtuka da neman gudunmawa don ginin karin ajujuwa da makarantar Alhuffaazh ta shirya a garin Saminaka.
Ya ce tuni Mai martaba Sarkin Lere Alhaji Abubakar Garba Muhammad, ya ba su kyautar wani babban fili, a garin Lere don gudanar da wannan aiki.
Ya ce dole sai mun samu goyon baya da hadin kan al’ummar wannan yanki kafin mu cimma wannan buri namu.
A jawabin Daraktan Makarantar Lauyoyi ta Najeriya Shiyyar Kano Dokta Nasiru Usman, cewa ya yi irin wadannan makarantu na koyar da ilimin addini da na boko suna da matukar amfani wajen samar wa al’umma ilimi mai tasiri. Ya ce cire harkar addini a cikin harkokin ilimi shi ne yake sanyawa ake samar da al’ummar da ba ta da tasiri.
Daraktan ya ce “Mu al’ummar Musulmi Allah Ya tsara mana komai a rayuwarmu baki daya. Don haka duk lokacin da muka ce za mu cire addini a cikin rayuwarmu to mun shiga uku.”
Dokta Nasiru Usman ya ce al’amarin ilimi akwai hakkin gwamnati akwai na iyaye akwai na malamai akwai kuma na al’umma. Ya ce a yau idan aka dubi Musulmin Arewa suna cikin hadari, saboda rashin hadin kai wajen taimaka wa al’umma, saboda abin da za su iya yi da kansu sai su tsaya suna jiran gwamnati ta yi musu.
Ya ce a jiha daya a Yammacin kasar nan za a samu jami’o’i na Gwamnatin Tarayya da na jiha da na kungiyoyin addini sama da 10, amma a Arewa da wuya a samu jihar da take da jami’a uku.
Dokta Nasiru ya ce idan maganar kudi ne, idan mutanen Arewa suka bude jami’o’i da kananan makarantu za su samu kudin kuma su samu lada. Don haka ya yi kira ga gwamnatoci da al’ummar Arewa su tashi tsaye wajen bude makarantu tare da inganta harkokin ilimi.
A jawabin Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani, ya yaba kokarin da makarantar Alhuffaazh take yi wajen ilimantar da al’ummar yankin.
Ya ce kawo makarantar ba karamin taimaka wa yankin ya yi ba. “Don haka ya zama wajibi mu fito mu rungumi makarantar ta hanyar sanya ’ya’yanmu a cikinta,” inji shi.
Tun da farko a jawabin shugaban makarantar Malam Misbahuddeen Hamza ya ce an shirya taron ne, domin bayar da kyaututtuka ga daliban da suka yi fice da kuma neman gudunmawa don karin ajujuwa a makarantar.
Ya ce sun samar da bas guda biyu don jigilar daliban makarantar zuwa da komowa gidajensu. Ya ce saboda kokarin da makarantar take yi, yanzu suna samun dalibai daga kowane sashi na kasar nan.