‘Cibiyar City Honda ta fara koya wa matasa 500 sana’o’i a Bauchi’
Cibiyar City Honda da ke koya wa matasa sana’o’i ta fara koya wa matasa 500 sana’o’i a Bauchi. Shugaban cibiyar Honarabul Umar Faruk Adamu ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Wakilin Aminiya a ranar Talata.Ya ce: “A yanzu mun dauki matasa 500 don koya musu yadda ake gyaran mota da babur da […]
Cibiyar City Honda da ke koya wa matasa sana’o’i ta fara koya wa matasa 500 sana’o’i a Bauchi.
Shugaban cibiyar Honarabul Umar Faruk Adamu ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Wakilin Aminiya a ranar Talata.
Ya ce: “A yanzu mun dauki matasa 500 don koya musu yadda ake gyaran mota da babur da kuma yadda ake sayar da kayayyakin gyaransu. Mun lura matasa da yawa a kasar nan ba su da wani aiki sai shan miyagun kwayoyi da sace-sace, inda muka fahimci rashin aikin yi ne ya sanya suke aikata miyagun dabi’u.”
Ya ce tun lokacin da aka kafa cibiyar shekara 25 da ta gabata sun yaye dimbin matasan da a yanzu suka dogara da kansu.
Ya ce za su ci gaba da amfani da kafafen yada labarai don wayar da kan matasa game da matakan da ya kamata su dauka wajen gyara halayensu.
A karshe ya bukaci gwamnati ta kokarta wajen samar wa matasa aikin yi don magance matsalar tsaro.