Cibiyar KbC: Abin Koyi Don Bunkasa Al’umma
A wannan zamani da al’amura suka tabarbare kuma suke ta ci gaba da tabarbarewa, lokacin da al’umma ke kara shiga matsaloli iri daban-daban. A wannan zamani da tattalin arzikin kasa ke kara shiga garari, lokacin da mafi yawan al’umma suka raja’a ga gwamnati domin neman abin rayuwa. Zamanin da talauci ke kara shiga sakade da […]
A wannan zamani da al’amura suka tabarbare kuma suke ta ci gaba da tabarbarewa, lokacin da al’umma ke kara shiga matsaloli iri daban-daban. A wannan zamani da tattalin arzikin kasa ke kara shiga garari, lokacin da mafi yawan al’umma suka raja’a ga gwamnati domin neman abin rayuwa. Zamanin da talauci ke kara shiga sakade da lungunan birane da karkararmu, zamanin da ayyukan yi da sana’a suka yi karanci, wanda haka ya sanya a duk shekara jami’o’i da kwalejoji suna yaye dubban daliban da kan zauna babu aiki ba sana’a. A wannan zamani da matasa ke kara shiga halayen shaye-shaye da aikata miyagun ayyuka, lokaci ne da al’umma ke tsananin bukatar tallafi. Lokaci ne da al’umma ke neman madogara domin sassaita al’amura.
Ganin irin tsananin bukatar da al’umma ke da ita na neman mafita, dalili ke nan a cikin watan Afrilu na shekarar 2002, Malam danjuma Katsina ya kirkiri cibiyar tallafa wa matasa da bunkasa al’umma mai zaman kanta, wacce ta samu tagomashin fitaccen mai kishin al’umma, Alhaji Muhammad Dikko Yusuf, tsohon Sufeto Janar Na ’Yan Sandan Najeriya. Tun daga lokacin kuwa cibiyar, wacce aka rada wa suna KbC (Katsina bocational Centre) ta shiga fafutukar yi wa al’umma hidima, wadanda suka hada da koyar da matasa sana’o’i da gudanar da laccocin fadakarwa da zaburar da al’umma domin su san inda ke musu ciwo.
Cibiyar ta fara ne da zakulo matasa, wadanda ta ga suna gararamba, sun gama makaranta amma babu aikin yi. Babu abin da suke yi sai shaye-shaye da zaman kashe wando. Irin matasan da suka zama alakakai cikin al’umma, suna fadace-fadace da juna. Cibiyar ta tace wasu daga cikinsu ta killace su, ta rika koya musu sana’o’i, kamar aikin kafinta, walda, dinki, saka, rini, gyaran famfo da sauran sana’o’in hannu. A duk shekara kuma cibiyar tana hada taro domin bikin yaye daliban da aka horar, inda ake yi musu jawaban karfafa gwiwa da ba su tallafin jari da kayan aiki domin ci gaba da sana’o’in da suka koya.
Ga matasan da tabarar shaye-shayen muggan kwayoyi ta yi wa kanta kuwa, cibiyar KbC ta yi nazari na musamman, ta shirya hanyoyin ceto su daga halaka. Cibiyar ta dauki matasa da muhimmanci a rayuwar al’umma, domin kuwa su ne shugabannin al’umma na gobe. Idan kuwa aka bari rayuwarsu ta gurbace, to al’ummar da za ta zo baya za ta zama gurbatatta. Dalili ke nan ya sanya cibiyar ta hada gwiwa da Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun kwayoyi (NDLEA), inda ake killace irin wadannan matasa, ana koya musu sana’o’in hannu tare da gabatar masu da hudubobin gyara musu tarbiyya. Irin wadannan matasa, an yi nasarar koya musu ilimin sarrafa kwamfuta da sana’ar hada turare da dinki da rini da sauran sana’o’in hannu makamantansu. Haka abin yake a kowace shekara kuma a kowane lokaci. Yawan matasan da aka ceto ta hanyar wadannan shirye-shirye, Allah Ya yi yawa da su, wanda haka ya sanya har ma da yawa daga matasan sun shiga taitayinsu, sun kintsu, sun daina irin wadannan shaye-shaye.
Gidajen yari, wurare ne da ake samun taruwar matasa masu gurbatattun halaye, wadanda suka aikata laifuka daban-daban. A irin wadannan wurare, abu ne mai muhimmanci a ce ana samun matakai da tsare-tsaren da za su sassaita tarbiyya da halayen mazauna cikinsu. Idan ba a gudanar da irin wadannan shirye-shirye na tsarkake halaye ba, babu shakka akwai yiwuwar maimakon gyara tarbiyya, matashin da ya samu kansa a irin wannan wuri ya kara samun gogewa ta fannin ayyukan assha. Domin ganin haka ba ta faru ba, cibiyar KbC ta yi hadin gwiwa na musamman da Hukumar Gidajen Yari na Katsina, inda ta rika tallafawa wajen koya wa fursunoni sana’o’in hannu, kamar dinki, saka da sauransu. Haka kuma, cibiyar ta rika ba da gudunmowar littattafai da kayan koyarwa, domin dai a samu nasarar wannan manufa ta tsarkake halaye da dabi’un fusrunonin, domin su zama nagari.
Ganin irin yadda ake tsananin bukatar cibiyoyi da kungiyoyin sa-kai a lungu da sakon birane da kauyukan Jihar Katsina, Cibiyar KbC ta fito da tsarin bayar da shawarwari ga masu son kafa kungiyoyi da cibiyoyin sa-kai. Ta haka kuwa an samu yaduwa da kafuwar kungiyoyi masu yawa, wadanda su ma suka rika gudaar da ayyukan cin gaba ga al’umma.
Ta fannin tarukan fadakarwa da yaye dalibai kuwa, a duk shekara cibiyar takan gudanar da gagarumin taro, inda take gayyatar masana da shugabannin al’umma, wadanda ke gabatar da jawabai da laccoci masu ma’ana ga al’umma. Irin wannan taro ya fara gudana ne a 2002, inda Babban Bako Mai Jawabi ya kasance Mai Shari’a Musa danladi Abubakar, wanda ya gabatar da lacca mai taken ‘Gudunmowar Matasa Wajen Bunkasa Al’umma.’ A 2003 kuma sai Farfesa Abdalla Uba Adamu na Jami’ar Bayero Kano ya zama Babban Bako Mai Jawabi, wanda ya gabatar da jawabi dangane da ‘Matsalolin Da Matasa Ke Fuskanta Na Rashin Aikin Yi Da Sana’o’i.’
Irin wannan taro ya gudana a 2004, inda Dokta Yusuf Nadabo Kaduna (Sarkin Tudun Nupawa) ya gabatar da jawabi mai taken: ‘Gudunmowar Matasanmu Ga Al’umma.’ A 2005 kuwa, a irin wannan taro, marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar-aduwa ne (lokacin yana matsayin Gwamnan Jihar Katsina) ya gabatar da jawabi mai taken: ‘Matasa: Matsalolin Rashin Aikin Yi, Shaye-Shaye da Yadda Za A Magance Su.’
A jere, tun daga 2006 zuwa 2013, muhimman mutanen da suka halarci taron na shekara-shekera kuma suka gabatar da jawabai masu amfani ga al’umma sun hada da Farfesa danjuma Maiwada da Malam Nuhu Ribadu da Mai Shari’a Ummaru Abdullahi da Hajiya Farida Waziri da Alhaji Sanusi Lamido Sanusi (Sarkin Kano na yanzu) da kuma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema. A bana, irin wannan taron zai gudana ne a ranar Talata, 18 ga watan nan, inda Sardaunan Katsina, Alhaji Ibrahim Coomassie zai kasance Babban Bako Mai Jawabi, kuma zai gabatar da jawabinsa mai taken ‘Yadda Matashi Zai Zama Dattijon Kirki.’
A lokacin da Cibiyar KbC ta cika shekara goma sha daya da kafuwa, idan muka waiwaya baya, muka yi la’akari da irin dinbin gudunmowar da take bayarwa wajen bunkasa al’umma, lallai sai mu ce Allah-san-barka!
***
Jinjina Ga Dokta Hassan Musa danbaba
Mun samu wannan sako ne daga wani yaro mai karanta Aminiya, mai suna ABDULWAHAB KABIR YAHUZA FUNTUWA, wanda ya aiko da cewa: “Gizago, don Allah ka mika mini sakon godiya da jinjina ga Dokta Hassan Musa danbaba, likitan Asibitin dandutse Sokoto Byepass Funtuwa. Abin sha’awa ne yadda wannan likitan ke gudanar da aikinsa cikin tausayi, yake iyakar kokarinsa ba tare da gajiyawa ba wajen ceton rayuka. Akwai wata rana wata majiyaciya aka rasa wanda zai taimake ta da jini, sai shi ya ba da nasa jinin aka diba kuma aka kara mata. Allah kara maka basira kuma ya biya ka, amin.”