Cibiyar koya wa matasa sana’o’i za ta yaye matasa 1,500 a Katsina

Cibiyar koya wa matasa sana’o’i (Katsina bocational Centre -KbC) za ta gudanar da bikin yaye dalibai 1,500 wadanda aka koya wa sana’o’i daban-daban a Katsina.Kamar yadda takardar sanarwa, wacce Daraktan Cibiyar, Malam danjuma Katsina ya aiko wa Aminiya ta nuna, za a gudanar da bikin ne a ranar 7 ga Satumba na bana. Daraktan ya […]

Cibiyar koya wa matasa sana’o’i za ta yaye matasa 1,500 a Katsina

Gwamna Ibrahim Shehu Shema na Jihar KatsinaCibiyar koya wa matasa sana’o’i (Katsina bocational Centre -KbC) za ta gudanar da bikin yaye dalibai 1,500 wadanda aka koya wa sana’o’i daban-daban a Katsina.
Kamar yadda takardar sanarwa, wacce Daraktan Cibiyar, Malam danjuma Katsina ya aiko wa Aminiya ta nuna, za a gudanar da bikin ne a ranar 7 ga Satumba na bana. Daraktan ya ce an koyar da matasan ne sana’o’i da ayyukan hannu da suka hada da dinki da saka da kimiyyar sarrafa kwamfuta da gyaran waya da rini da walda da sarrafa sabulu da sarrafa man shafawa da sauransu.
“A shekarun da suka gabata, mun yaye dubban dalibai maza da mata, wadanda suka koyi sana’o’i daban-daban; wadanda kuma a yanzu haka suna gudanar da sana’o’in kansu, suna cin gashin kansu kuma suna koyar da wasu, kamar kuma yadda suke samar da ayyukan yi ga wasu.” Inji danjuma Katsina.
A bikin cibiyar na bana, bayan yaye daliban kuma za a rarraba kayayyakin aiki ko na sana’a ga gajiyayya da kuma mata da suka koyi sana’o’i daga cbiyar ta Katsina bocational Training Centre.
Manyan baki da za su halarci bikin sun hada da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, a matsayin babban bako mai jawabi.
A shekarun da suka gabata, a yayin bikin cibiyar ta KbC, wacce tsohon Sufeto-Janar M. D. Yusuf ya kafa, fitattun mutanen da suka gabatar da jawabai sun hada da Sanusi Lamido Sanusi da Malam Nuhu Ribadu da Farida Waziri da Farfesa Abdullahi Uba Adamu da Mai shari’a Umaru Abdullahi da sauransu.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna