Cibiyar MCRP ta bai wa ‘yan gudun hijira horo kan sasanta rikici
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno, Alhaji Abdulkarim Lawan ya yaba wa Cibiyar Ayyukan Farfado da Yankunan da Rikici ya Shafa ta MCRP saboda bayar da horo ga masu ruwa da tsaki na garuruwan da fadan Boko Haram ya shafa kai tsaye. Ya yi yabon ne a ranar Juma’a 2 ga watan Nuwamban shekarar 2018 yayin […]
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno, Alhaji Abdulkarim Lawan ya yaba wa Cibiyar Ayyukan Farfado da Yankunan da Rikici ya Shafa ta MCRP saboda bayar da horo ga masu ruwa da tsaki na garuruwan da fadan Boko Haram ya shafa kai tsaye. Ya yi yabon ne a ranar Juma’a 2 ga watan Nuwamban shekarar 2018 yayin da yake bude taron sanin makama na kwanaki uku kan sasanta rikici a tsakanin garuruwan da rikicin Boko Haram ya shafa a Kananan Hukumomi 10 na Jihar. Lawan ya ce shirin ba wai kawai yana da muhimmanci ba har ya zama wajibi tun da tuni mutane suka fara komawa garuruwansu.Ya bayyana cewa yayin da mutane suka dawo abubuwa da yawa za su taso sakamakon rikicin Boko Haram wanda idan ba a dauki matakin da ya dace ba zai iya tayar da wani rikici a tsakanin al’umma.
Shugaban Majalisar ya bayyana cewa irin wannan horo kan sasanta rikici zai taimaka kwarai da gaske wajen tabbatar da zaman lafiya da dorewarsa da walwala a tsakanin wadanda suka dawo tare da kare aukuwar kashe-kashe da zubar da jini da asarar dukiya. Ya lura cewa zaman lafiya shi ne ginshikin bunkasar tattalin arziki sannan kuma ya yi fatan sauran garuruwa a sauran kananan hukumomin jihar za a shigo da su cikin shirye-shiryen da ke gaba.
Tun farko Manajan Shirye-shirye kuma kwandinetan Ayyuka na Cibiyar Ayyukan Farfado da Bangarorin da Rikici ya Shafa a Jihar Borno, Baba Zanna Abdulkarim ya kawo tarihin yadda taron bayar da horon ya fara a shekarar 2015 lokacin da Jihar ta fara samun kwarya-kwaryar zaman lafiya a wasu garuruwa. Ya ce taron bitar yana daya daga cikin burin da Cibiyar MCRP take son cimma wacce ta mayar da hankali wajen tabbatar da samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomi tare da farfado da al’ummar wadannan garuruwan wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.
Kwandinetan Ayyukan ya bukaci wadanda suke samun horon su zama jakandun zaman lafiya kuma masu yada zaman lafiya sannan ya tunatar da su cewa ana bukatar su yi amfani da duk hanyoyin da suka dace wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a. Ya bayyana cewa Cibiyar MCRP da Bankin Duniya na World Bank suna baiwa sasanta rikici muhimmanci saboda haka akwai bukatar wadanda suka samu horon su yi amfani da wayoyin tarho da aka bayar don amfanin al’ummominsu.
A bangarensa Babban Mai Bayar da Horo, Farfesa Ibrahim Umara na Jami’ar Maiduguri ya ce an zabo kimanin mutum 500 daga kananan hukumomi 10 daga sassa uku na Jihar don su shiga shirin na kwanaki uku. Bayan samun horon za su kasance manyan masu ruwa da tsaki a garuruwansu kuma a na son su kasance jakadun tabbatar da zaman lafiya da magance fargaba da tashin hankali da zai iya tasowa bayan rikicin Boko Haram.
Farfesa Umara ya kara da cewa gudanar da shirin bayar da horon a cibiyoyi biyu a lokaci guda a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ramat da Kwalejin Ilimi ta Maidugiri ya auku ne don tabbatar da wadanda aka zabo sun sami horo mai inganci. Yayin da yake yaba wa Gwamna Kashim Shettima saboda jajircewarsa wajen tabbatar da komawar jama’a lafiya ya yaba wa wadanda ke bayar da horon da suka zabi su bayar da horon a Harshen gida.
Cibiyar MCRP wani shiri ne na shekaru biyar wanda Gwamnatin Tarayya ta hannun Kwamitin Sake Gina Yankin Arewa maso Gabas na PCNI da Bankin Duniya na World Bank da Gwamnatin Jihar Borno da Adamawa da Yobe suka shirya. Zangon farko na shirin an kaddamar da shi ne a watan Satumba kuma don cimma burin karfafa ginin zaman lafiya da dorewarsa da walwala.