Cibiyar Republican ta shirya wa matasan Jam’iyyar APC bita a Abuja
Wata cibiya mai suna International Republican Institute (IRI), ta shirya bita a kan ayyukan siyasa ga matasan sabuwar Jam’iyyar APC, inda aka gudanar da laccoci da muhawara kan kalubalen siyasa ga matasan da suka fito daga sassan kasar nan a Abuja. Wadanda suka gabatar da laccocin sun hada da Babbar Daraktar cibiyar a Afirka mai […]

Wata cibiya mai suna International Republican Institute (IRI), ta shirya bita a kan ayyukan siyasa ga matasan sabuwar Jam’iyyar APC, inda aka gudanar da laccoci da muhawara kan kalubalen siyasa ga matasan da suka fito daga sassan kasar nan a Abuja.
Wadanda suka gabatar da laccocin sun hada da Babbar Daraktar cibiyar a Afirka mai hedikwata a Afirka ta Kudu Misis Robina Namusisi da tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da Injiniya Buba Galadima da Cif Audu Ogbe da kuma Shugaban Matasan Jam’iyyar APC, Alhaji Lado Suleja.
A jawabin Misis Namusisi ta ce Cibiyar IRI za ta taimaka wa jam’iyyar da sauran sababbin jam’iyyun siyasa wajen wayar da kai da kuma muhimmacin jawo wadanda ba a yi da su a jika, kamar mata da matasa.
A jawabin Cif Audu Ogbe ya koka da yanayin da matasan kasar nan suka samu kansu a ciki na matsalar rashin aikin yi, wanda a sakamakon hakan inji shi, fitinu ke karuwa a cikin kasa.
Shi kuwa Malam Ibrahim Shekarau, ya ce malaman jami’a da ke yajin aiki a yanzu haka, ba su da hurumin sukan gwamnati na rashin cika alkawari da ta yi da kungiyarsu ta ASUU,
Ya ce da su aka hada kai aka yi wasu abubuwan Allah wadai a zaben da ya gabata, bayan Shugaban Hukumar Zabe Farfesa Attahiru Jega ya dauko su daga jami’a a matsayin turawan zabe a jihohi.
Shugaban Matasan Jam’iyyar APC ya bukaci matasan su yi tsayuwar daka wajen jawo hankalin jama’a tare da yi musu rajista a sabuwar jam’iyyar a matsayin matakin farko na kafa jam’iyyar a kan turbar nasara.