Cibiyar Sarki Salman ta yi rabon tallafin abinci a Kano

Muna fata nan gaba ma za su sake kawo mana kwatankwacin irin wannan tallafi.

Cibiyar Sarki Salman ta yi rabon tallafin abinci a Kano

Cibiyar Jin-ƙai ta Sarki Salman bn Abdulaziz na Saudiyya, ta yi rabon tallafin kayan abinci ga mabuƙata 2,056 a Jihar Kano.

Cibiyar ta yi rabon tallafin mai taken “Kwandon Kayan Abinci” domin rage wa mabuƙatan raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fuskanta.

Daraktan Ayyuka na Musamman, Hajiya Fatima Kassim wadda ta yi jawabi a madadin Darakta Janar ta Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, ta bayyana cewa an raba tallafin ne domin taimaka wa al’umma da kuma rage musu raɗaɗin halin matsin da suke ciki.

A cewarta, kayayyakin abincin da aka raba wa mabuƙatan sun haɗa da buhuna shinkafa mai nauyin kilo 25 da buhunan wake mai nauyin kilo 25 da tumatirin leda guda 35 da ledar gishiri biyu da jakar garin semovita guda biyu da man girki lita ɗaya da sinadarin ɗanɗano leda biyu.

A nasa jawabin, wakilin Cibiyar Jin-ƙai, Abdurrahman Abdulazeez Alzabain ya bayyana cewa tallafin ya fito ne daga Gwamnatin Saudiyya a karkashin jagorancin Sarki Salman bn Abdulazeez domin tallafa wa Musulmin Duniya a wannan wata na Azumin Ramadana.

Da yake jawabi, Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya bayyana cewa tallafin ya zo ne a daidai lokacin da mutane ke cikin buƙata saboda azumin watan Ramadan da kuma halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

“Muna godiya ga wannan cibiya saboda wannan tallafi shi ne karo na uku da wannan cibiyar take yi ga Jihar Kano domin a bara ma ta raba wa masu buƙata ta musamman har su 500.

“Muna fata nan gaba ma za su sake kawo mana kwatankwacin irin wannan tallafi.”

Mataimakin Gwamnan ya kuma miƙa godiya cibiyar game da wannan tallafi da ta kawo Jihar Kano, yana mai cewa hakan yana manuniya ce da irin dadaddiyar alaƙar da ke tsakanin kasar Saudiyya da Najeriya da kuma Jihar Kano.

Ya kuma yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da irin wannan abu da cibiyar ta yi wajen ganin sun taimaka wa mutane da ke cikin matsanancin halin buƙatar taimako.

Wasu daga cikin waɗanda suka rabauta da tallafin, Bashir Ubale da Habiba Muhammad sun gode wa cibiyar ta Sarki Salman, inda suka yi alkawarin yin amfani da abin da suka samu ta hanyar da ta kamata.

An kama matashin da ya kashe yayansa da wuƙa a Kebbi

Za mu shirya Kwankwaso da Ganduje — Kofa

Harin jirgin soji a Zamfara: Ya kamata a biya mu diyya —Iyalai

Matatar Dangote ta kara farashin fetur zuwa N955