Cif Obasanjo: dan kishin kasa ko kishin kai?
A ranar Larabar makon da ya gabata aka samu bayyanar wasikar nan mai shafuffuka 18, ta ranar 2 ga wannan watan na Disamba, da tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa shugaba mai ci Dokta Goodluck Jonathan, mai taken “Kafin a makara.” Waccan wasika ta ja hankalin miliyoyin al`ummar duniya, musamman `yan kasar […]
A ranar Larabar makon da ya gabata aka samu bayyanar wasikar nan mai shafuffuka 18, ta ranar 2 ga wannan watan na Disamba, da tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa shugaba mai ci Dokta Goodluck Jonathan, mai taken “Kafin a makara.” Waccan wasika ta ja hankalin miliyoyin al`ummar duniya, musamman `yan kasar nan a duk inda suke, bisa ga la`akari da irin yadda aka san cewa tsohon shugaban kasar shi ne uban gidan siyasa na Shugaba Jonathan tun karatowar zabubbukan shekarar 2007, bayan batun “Tazarcensa” ya kare, inda ya hada tafiyar Gwamna Umaru Musa `Yar`aduwa na Jihar Katsina da Dokta Goodluck Jonathan Gwamnan Jihar Bayelsa, a zaman `yan takarar neman shugabancin kasa a inuwar jam`iyyar PDP (a zaman shugaba da mataimakinsa) a zabubbukan shekarar 2007.
Wasikar ta Cif Onasanjo ga shugaba Jonathan ta mayar da hankali ne akan irin halin da kasar nan take ciki na zamantakewa da tattalin arzikin kasa da harkokin siyasa. Alal misali Cif Obasanjo ya zangi shugaba Jonathan da ruru wutar siyasar kabilanci, ta yadda ba abinda ya sanya a gaba kuma bai jin maganar kowa sai ta `yan kabilarsa ta Ijaw, alhali inji wasikar tsohon shugaban kasar, shugaba Jonathan, ya manta da cewa dukkan al`ummar kasa nan suka kada masa kuri`a. Ya kuma zargi shugaba Jonathan da gwamnatinsa akan kasa tabuka kome wajen kawo karshen rashin tsaro da kusan dukkan sassan kasar nan suke ciki, yana mai nuni da rikicin `yan kungiyar Jama`atu Ahlis Sunnah Lid Da`awati Wal Jihad da ake wa lakabi da Boko Haram a Arewa da rikicin tsagerun Neja Delta na sace mutane da yin garkuwa da su da neman fansa da satar danyen man fetur, da uwa uba cin hanci da rashawa da suka yi kamari, a kusan dukkan harkokin gudanarwa na gwamnatin shugaba Jonathan.
Wani batu da wasikar ta tabo, shi ne na rikicin da jam`iyyar PDP ta fada, musamman da gwamnoninta biyar daga cikin bakwai da suke ta adawa da aniyar shugaba Jonathan na takarar zaben 2015, a inuwar jam`iyyarsu ta PDP da shugabancin jam`iyya na Alhaji Bamanga, gwamnonin da tuni suka fice daga cikin jam`iyyar ta PDP, suka koma APC. Wasikar ta zargi shugaba Johathan da kasa kawo karshen wannan rigima. Haka kuma wasikar ta zargi shugaba Jonathan da goyawa jam`iyyun adawa naya a jihohin Edo da Ondo da Anambra a zabubbukan gwamnonin jihohinsu, har suka kai ga nasara, ma`ana ya yi watsi da `yan takararar jam`iyyarsa ta PDP, da fatan idan Allah Ya kaimu zabubbukan shekarar 2015, wadancan gwamnonin jihohi zasu taimaka masa ya ci zaben.
Akan neman tsayawa takarar shugaba Jonathan a zaben 2015, wasikar ta Cif Obasanjo ta zargi shugaba Jonatahan da boye wa Cif Obasanjo gaskiyar lamari, inda wasikar ta bayyana cewa lokuta da dama idan shi ya tunkari shugaba Jonathan don jin ko zai tsaya takarar? Shugaba Johathan, ya sha fada masa cewa har yanzu bai yanke hukunci ba, alhali a gefe daya dukkan take-taken na kusa da shugaban kasar suna nuni da cewa shugaba Jonathan yana da wannan bukata. A irin wannan hali inji tsohon shugaban kasar, Dokta Jonathan ya turo shugabannin kasashe shidda wajensa da bukatar lallai ya taimaka masa a zabe mai zuwa.
Zarge-zargen da wasikar Cif Obasanjo ta yi akan shugaba Jonathan suna da yawa, sai dai a takaita, saboda rashin fili a wannan makala `yan wadannan kadai zan iya kawo ma mai karatu. Zarge-zargen da ya zuwa yanzu shugaba Jonathan ya bayyana su da cewa zancen banza ne da basu da tushe bare makama, sannan kuma ya hana dukkan wani babban jami`in gwamnatinsa da kar ya mayar da martini, da alkawarin shi da kansa zai mayar da martini idan lokaci ya yi. Duk da ya ke Cif Obasanjo ya ce a baya ya aika da irin wannan wasika ga shugaba Jonathan har sau uku da bai taba samun amsarsu ba.
Tarihi ya tabbatar da cewa tun da Cif Obasanjo ya bar gwamnatin mulkin soja a shekarar 1979, ya mika wa Alhaji Shehu Shagri mulki a zaman shuban kasa na farar hula, bai taba barin wata gwamnati ta sarara ba a kasar nan, irin wannan katsalandan din ne ya sanya a shekarar 1995, gwamnatin marigayi Janar San Abacha ta kama Cif Obasanjo a wani yunkurin juyin mulki, ta daure shi rai da rai, wanda sai bayan da Janar Abacha ya mutu ne a shekarar 1998, aka yafe wa Cif Obasanjo, aka kuma ba shi takarar shugabancin kasa a inuwar jam`iyyar PDP, inda ya kwashe shekaru takwas cur yana mulki.
Masu kula da al`amurran da kaje su zo a kasar nan, suna ganin ba don kishin kasa, Cif Obasanjo ya fito da wannan wasika a irin wannan lokiaci ba, illa kawai don dama halinsa ne, dadin-dadawa kuma don ya samu madafa akan zabubbukan shekarar 2015, akan dukkan wani dan takara da ya ka samu nasara, musamman na Arewacin kasar nan, ya yi da shi, don kuwa a dukkan batutuwan da ya zargi shugaba Jonathan da aikatawa, ba wadanda bai yi ba a lokacin mulkinsa na shekarun 1999 zuwa 2003, kama a iya cewa wajen gwamnatinsa shugaba Jonathan ya koyi wasu. Wanne ne ba wanne ne ba? Kama karya a cikin tafiyar da jam`iyya ne da ya yi zamani da shugabannin jam`iyya hudu da ya rika tubewa a duk lokacin da yake so, ko mured zabubbuka ne bai yi ba. Akan zargin tabarbarewar cin hanci da rashawa, ai kowa ya sa ni yakin da Hukumomin EFCC da ICPC suka rika yi, akan wadanda gwamnatin ta karya kara da su ne kawai Hukumomin biyu suka rika dirar mikiya.
A yar tawa fahimtar ba wai don kishin kasa Cif Obasanjo ya bayyana waccan takarda tashi ba, illa don kawai kamar yadda na ce sai don ya ci gaba da samun madafa, musamman daga mutanen kasar nan, musamman na Arewaci. Su kuma `yan Arewa kamata ya yi su himmatu wajen hada kansu wuri guda, a irin wannan lokaci da gwamnatin shugaba Jonathan take yin amfani da bambance-bambancen addini da kabila da ke tsakaninsu. Ga shugabanni masu tunkahon son su nada wani akan karagar mulki,ya kamata su sa ni cewa, duk wanda ya hau kan karagar mulki ba mai son a ce wani daga waje ke juya shi, koda kuwa mahaifinsa ne, musamman irin wannan zamani da muke ciki, don haka su rika hakuri, su kuma bar mai mulki ya yi mulkinsa, ta haka ne kawai mulkin demokradiyyar da muke kai zai daukaka.