Cika baki ne ya jawo gazawar PDP – Tsohon Gwamna
Tsohon Gwamnan Jihar Neja Injiniya Abudulkadir Abdullahi Kure ya nemi afuwar al’ummar jihar bisa kura-kuran da Jam’iyyarsu ta PDP ta tafka a tsawon shekara 16 tana jan ragamar mukin Najeriya da jihar, wadanda suka jefa talakawa cikin mawuyacin hali a yau.Injiniya Abdulkadir Kure ya nemi afuwar ce a Kwantagora yayin kaddamar da kamfen din ’yan […]
Tsohon Gwamnan Jihar Neja Injiniya Abudulkadir Abdullahi Kure ya nemi afuwar al’ummar jihar bisa kura-kuran da Jam’iyyarsu ta PDP ta tafka a tsawon shekara 16 tana jan ragamar mukin Najeriya da jihar, wadanda suka jefa talakawa cikin mawuyacin hali a yau.
Injiniya Abdulkadir Kure ya nemi afuwar ce a Kwantagora yayin kaddamar da kamfen din ’yan takarar shugabannin kananan hukumomi da za a yi a gobe Asabar.
Tsohon Gwamnan da yake tuna irin abin da ya same su a zabubbukan da aka gudanar a bara, inda Jam’iyyar PDP ta sha kaye ya danganta lamarin da muguwar rawar da shugabanni suka taka a matakai daban-daban.
Ya ce, “Ina nadamar tsayuwa a gabanku a matsayinmu na ’yan adawa a halin da muka samu kanmu a yau. Shekarun baya mun bugi kirjin cewa sai mun shafe shekara 60, PDP na mulkin Najeriya. Allah cikin ikonSa Ya nuna mana cewa Shi Yake da iko a kan komai inda Ya karbe mulki daga hannunmu Ya ba ’yan adawa na wancan lokacin.”
Ya yi kira ga jama’a su yi hakuri su fito kwansu da kwarkwata su zabi ’yan takarar Jam’iyyar PDP a gobe Asabar cikin natsuwa da martaba dokoki domin a samu nasarar ci gaban yankunan karkara.
Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Neja, Malam Umar Musa Ma’ali wanda ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar za ta lashe ilahirin kujerun shugabannin kananan hukumomin da kansilolin a zaben da ke da matukar tasiri ga mazauna yankunan karkara.
Malam Umar Ma’ali ya kara da cewa, “Jama’a kowa yana ji a jikinsa daga lokacin da jam’iyya mai ci ta amshi mulki daga hannunmu al’amura suka ci gaba da tabarbarewa, wannan ya sa tun ba a je ko’ina ba ’yan Najeriya suke ganin tasku. Jama’a na fama da dogayen layuka a gidajen mai, ga fannin tattalin arziki ya kara tabarbarewa. Irin wannan alkawarin ne aka yi muku lokacin kamfe a baya?”