Cikakken Bafulatani ba ya sata — Sanata Bayero

Tsohon Sanatan ya ce wasu ne ke shiga rigar Fulani suna ɓata musu suna.

Cikakken Bafulatani ba ya sata — Sanata Bayero

Tsohon Sanata mai wakilitar Gombe ta Arewa, Sanata Usman Bayero Nafada, ya ce cikakken Bafulatani na asali ba ya aikata sata, bare aikata laifukan ta’addanci.

Sanatan, ya bayyana haka ne a wajen bikin al’adun Fulani na Duniya Na Pulaaku da gamayyar ƙungiyoyin Fulani na FUDECO da GAM ALLAH, Dan Miyyetti Allah suka shirya a Gombe.

Ya ce wasu na ɓata sunan Fulani, amma tun asali ƙabilar ko roƙo ba a san su da yi ba bare aikata sata.

“Wasu ne suka shiga rigar Fulani suke satar mutane, suke hana manoma aikin gona shi ne ake musu kallon Fulani,” in ji Bayero.

Tsohon Sanatan wanda shi ne uban ƙungiyar FUDECO a Jihar Gombe, ya shawarci jama’a da su dai na ɓata wa Fulani suna, domin ba su ke aikata ayyukan ta’addanci ba.

An gudanar da bikin kamar yadda aka saba domin nina al’adun gargajiya don haɗa kan Fulani a jihar da ma maƙwabtansu.

Ya kuma shawarci kwamitin shirya taron da suka gayyato wasu ƙabilun irin su Tangalu, Terawa, Bolawa da sauransu don taya su bikin, kasancewar ƙabilun kan gayyace irin nasu bikin.

A yayin bikin an yi bajakolin kayayyakin al’adu da suka shafi ƙawa, kwalliya, abinci da sauransu.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC