Cikakken jadawalin rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026
Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta kammala fitar da jadawalin Rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026.
- Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike
- DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara
Rabon jadawalin ya gudana ne a birnin Washington na ƙasar Amurka a ranar Juma’a, inda Ingila ta samu kanta a rukuni ɗaya Croatia.
Brazil za ta kara da Maroko, yayin da Amurka za ta kara da Australia.
Faransa za ta ɓarje gumi da Senegal, sannan Argentina za ta fafata da Austria.
Ga jerin yadda kowane rukuni na gasar Kofin Duniya na 2026 ya kasance:
Rukuni A: Mexico, Afirka ta Kudu, Koriya ta Kudu, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar.
Rukuni B: Kanada, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Qatar, Switzerland
Rukuni C: Brazil, Maroko, Haiti, Scotland
Rukuni D: Amurka, Paraguay, Australia, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar.
Rukuni E: Jamus, Curaçao, Ivory Coast, Ecuador.
Rukuni F: Netherlands, Japan, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Tunisia.
Rukuni G: Belgium, Masar, Iran, New Zealand.
Rukuni H: Spain, Cape Verde, Saudi Arabia, Uruguay
Rukuni I: Faransa, Senegal, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Norway
Rukuni J: Argentina, Aljeriya, Austria, Jordan.
Rukuni K: Portugal, ƙasar da ta samu gurbin zuwa gasar, Uzbekistan, Colombia
Rukuni L: Ingila, Croatia, Ghana, Panama