Cikar Sarkin Jama’a shekara 20 a kan karaga (2)
An haifi Mai martaba Sarkin Jama’a na 11, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II a garin Kafanchan ranar 18 ga watan Yunin 1970, kuma shi ne da namiji na farko ga marigayi Sarkin Jama’a Alhaji Isa Muhammad. Ya girma a gaban mahaifansa a cikin fada. Ya fara karatun allo a makarantar Malam Tanko Jama’a a 1973. […]
An haifi Mai martaba Sarkin Jama’a na 11, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II a garin Kafanchan ranar 18 ga watan Yunin 1970, kuma shi ne da namiji na farko ga marigayi Sarkin Jama’a Alhaji Isa Muhammad.
Ya girma a gaban mahaifansa a cikin fada. Ya fara karatun allo a makarantar Malam Tanko Jama’a a 1973. Ya kuma yi karatun addini Musulunci. Ya shiga makarantar firamare a 1975 a makarantar da yanzu ake kira “Waziri Aliyu Primary School” daga nan ya wuce makarantar sakandaren GSS Kafanchan inda ya kammala a 1986.
A 1987 ne ya wuce makarantar Share Fagen Shiga Jami’a (CAS) da ke Zariya daga nan ya shiga Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna (Federal Polytechnic) wacce ya kammala a 1992.
An nada shi a matsayin Magajin Garin Jama’a a 1991, yayin da shekara daya bayan nan, a 1992 aka nada shi Hakimin Kafanchan. Wannan ne ya ba shi damar ci gaba da taimaka wa mahaifinsa tare da koyon dabarun mulki a wajensa.
Ya zama Sarki ne yana da shekara 28 a duniya.
Kalubale da nasarori
Rikice-rikicen kabilanci da na addini da na siyasa na daga cikin manyan kalubalen da Mai martaba Sarkin Jama’a ya fara fuskanta tun farkon hawansa gadon sarauta amma cikin ludufin Allah da kwarancewa wajen tafiyar da mulki, sannu a hankali aka fice daga cikinsu daya bayan daya, kamar yadda Kuyambanan Jama’a ya shaida wa Aminiya.
“Tun daga ranar ba shi sanda a 1999 aka fara rikice-rikice amma alhamdulillahi zuwa yanzu an samu zaman lafiya sosai. Masarautar Jama’a akwai kabilu wadanda su ke ba Musulmi ba da ke zaune a cikinta da kuma wadanda ke kewayenta kuma kowanne na gudanar da harkokin addininsa ba tare da tsangwama ba.
Babu shakka an samu ci gaba da nasarori masu yawa cikin shekara 20 da hawa sarauta na Alhaji Dokta Muhammad Isa Muhammad domin a lokacinsa ne aka samu fitattun ’yan siyasa da mashahuran ’yan kasuwa a masarautar,” inji shi.
Shi ma shugaban cocin Anglikan na Kudancin Kaduna da ke Kafanchan, Bishop Markus Dogo ya bayyana Sarkin Jama’a a matsayin shugaba abin koyi wajen tafiyar da jama’arsa ba tare da nuna bambanci ba, inda ya ba da misali da cewa: “A irin rikice-rikicen da aka yi a lokutan baya akwai lokacin da aka sanya wa coci wuta, bayan na samu labari wallahi waya kawai na daga na shaida masa nan da nan sai ya turo mutanensa Musulmi suka zo suka kashe wutar, ka san cocin na karkashin masarautarsa ce.”
Shi ma Fasto Kure, mamallakin cocin Good News da ke karkashin Masarautar Jama’a a garin Kafanchan ya bayyana Sarkin a matsayin shugaba mai adalci da ba ya goyon bayan ta da fitina inda ya kawo misali da yadda matasan masarautar ke zuwa don ba cocinsa kariya a lokacin rikici.
Shi ma da yake bayyana irin nasarorin da masarautar Jama’a ta samu a karkashin Sarki Muhammadu Isa Muhammad, Dan Madamin Jama’a Alhaji Aminu Isa Muhammad ya ce, masarautar, a karkashin mulkin yayansa ta samu gagarumin ci gaba da suka hada da samun zaman lafiya da gudanar da mulki ba tare da nuna bambanci ba da tsayin dakan da ya yi wajen samun barikokin sojoji da na ’yan sandan kwantar da tarzoma.
“Kuma a lokacinsa ne aka samu reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) a garin Kafanchan. Shi ne wanda ya jagoranci sake gina babban masallacin Juma’a na Kofar Fada wanda ya isa abin nunawa a ko’ina a Najeriya. Kuma a zamaninsa yanzu haka ake sake gina babbar kasuwar Kafanchan,” inji shi. Sannan ya bayyana yadda Sarkin ya yi kyakkyawan mu’amala da gwamnatocin mulkin soja da na farar hula ba tare da samun matsala da kowa ba.
Lambobin yabo
A shekarar 2002 ce Gwamnatin Tarayya a karkashin mulkin tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ta ba shi lambar girmamawa ta OFR, inda kafin nan yake dauke da lambar girmamawa na FICEN.
Ya sake samun lambar girmamawa ta CON a lokacin mulkin Dokta Goodluck Jonathan yayin da Jami’ar Atlantic American Unibersity da ke Jihar Anambra ta karrama shi da digirin digirgir na girmamawa (Dokta).