Cikar Sarkin Kano Shekara 50: Tun Ado Bayero yana karami muka ga alamun shugabanci a tare da shi -Hadiza Bayero

A karshen makon da ya gabata ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya yi bikin cika shekara 50 a kan karagar mulki.  Wakiliyarmu ta tattauna da wadansu na kusa da Sarki game da rayuwarsa.daya daga cikin kannen Sarkin  Kano Alhaji Ado Bayero, Hajiya Hadiza Bayero ta bayyana cewa dama tun farkon rayuwar Mai […]

Cikar Sarkin Kano Shekara 50: Tun Ado Bayero yana karami muka ga alamun shugabanci a tare da shi -Hadiza Bayero
Cikar Sarkin Kano Shekara 50: Tun Ado Bayero yana karami muka ga alamun shugabanci a tare da shi -Hadiza Bayero

A karshen makon da ya gabata ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya yi bikin cika shekara 50 a kan karagar mulki.  Wakiliyarmu ta tattauna da wadansu na kusa da Sarki game da rayuwarsa.
daya daga cikin kannen Sarkin  Kano Alhaji Ado Bayero, Hajiya Hadiza Bayero ta bayyana cewa dama tun farkon rayuwar Mai martaba Sarkin Kano ya nuna alamun shugabanci,  idan aka yi la’alkari da halayyarsa ta son jama’a da farin jini da kuma kyauta ga jama’a .
 Hakan ce, inji ta, ya sanya a lokacin da aka yi masa sarautar Sarkin Kano kowa ya yi na’am tare da nuna gamsuwa. “Da ma tun farko Allah Ya nuna cewa Mai martaba zai zama wani abu a rayuwarsa, don dai mutum bai san gaibu ba ne. Shi mutum ne mai son yara, ga kuma farin jinin jama’a, duk inda ya sa kafa sai ka gan shi da jama’a,  haka kuma ga hannun baiwa. Duk da cewa muna baya da shi amma ina iya tunawa a wancan lokaci haka yake rarraba mana kobo da dari. Haka kuma idan wata matsala ta ki warwaruwa a cikin dangi, to da an kawo ta gabansa yanzu kuwa zai warware ta.” Inji ta.  
Hajiya Hadiza Bayero wadda ta yi wannan bayanin ga Aminiya, ta kara da cewa, “Lokacin da aka nada shi a matsayin sarki duk da cewa akwai na gaba da shi sosai, dukkaninmu ‘yan uwansa babu wanda bai yi farin ciki ba, kasancewar mun san cewa zai iya rike wannan mukami da Allah Ya ba shi. A karshe ina yi wa sarki addu’ar karasa ragowar kwanakin da suka rage masa a kan mulki lafiya.”
Shi ma wani daga cikin wadanda suka gudanar da kuruciya tare da Sarki mai suna Alhaji Garba,  wanda a yanzu haka yana daya daga cikin manyan yaran Sarki, ya bayyana cewa kasancewar shi ma ya taso a gidan Sarki sakamakon mahaifinsa da yake a matsayin dan morin Sarkin Kano Abdullahi Bayero,wato mahaifin Sartki Ado Bayero, ya bayyana Sarkin Kano Ado da cewa mutum ne mara girman kai, domin shi kowa nasa ne, da dan sarauta da dan attajiri da dan talaka duk daya ne a wurinsa. “Kasancewar mun rayu a wuri daya , duk da cewa akwai bambancin shekaru a tsakaninmu, domin na girmi Sarki Ado Bayero da shekaru hudu, a wancan lokaci tare muke wasa. Babu shakka Sarkin Kano mutum ne wanda ba shi da girman kai, babu ruwansa da nuna bambanci tsakanin ‘ya’yan manya da na talakawa, kowa nasa ne. Tun da ya tashi mutum ne shi kamili mai girmama na gaba da shi. Haka kuma mutum ne mai gaskiya. Kai in takaice miki, ba za a samu dan sarki Kamar Ado Bayero ba. Tun yana yaro shi mutum ne mai kyauta da son mutane da kuma farin jinin jama’a. Ina iya tunawa a lokacin da yake aiki a banki na kan je na ziyarce shi a banki na gaishe shi, har ma ya yi min kyauta. “     
Dangane da yadda aka nada Sarki kuwa Alhaji Garba cewa ya yi, “Duk da cewa ba ma tare wancan lokacin, domin ni daga baya Bichi aka mayar da ni wajen yayan Sarkin dan iya Aminu. muna can muka samu labarin an nada Sarki Ado Bayero a lokacin shi kansa yana matsayin jakada a kasar Senegal, sai daga baya muka zo cikin gari aka gudanar da bikin nadinsa, inda aka yi shagulgula da dama da suka hada da kade-kade da raye-raye da sauransu.” Inji shi.
Alhaji Garba ya bayyana Sarki da cewa mutum ne mai hangen nesa, kuma ba ya zartar da hukunci ba tare da ya yi bincike ba.  “A lokuta da dama idan aka zo masa da wata magana a kan wani hakimi ko dagaci ya kan tsaya ya yi tunanin sosai a kan maganar tare da yin bincike sosai. Idan ya kama abin na ladabtarwa ne zai yi kiran mai laifin ya yi masa nasiha tare da nuna masa abin da ya kamata ya yi. Kafin ka ga Sarki ya tube wani shugaba a kan kujerarsa , sai abin ya kai intaha, ta yadda ba zai warwaru ba.  Da wuya ya raba mutum da hanyar cin abincinsa. Haka kuma  shi mutum ne da ba shi da riko.”
Shi ma Abdulkadir Sani Dogari wanda shi ne Mukaddashin Dogarai, ya bayyana cewa, yana matsayin dogari a lokacin da Sarki Ado Bayero ya zama Sarki, ya ce irin shaguglgulan da aka gudanar a lokacin nadin Sarkin sun faru ne saboda irin farin jinin sarkin da kuma irin kaunar da jama’a ke yi wa sarkin.
Babbar Jakadiyar Sarki mai suna Adama Musa, wacce ta ce ta shafe tsawon shekaru 37  a cikin gidan sarkin, ta bayyana cewa ba ta taba ganin bacin ran sarkin ba , sai dai halayyarsa ta kulawa da jama’a da kuma kyauta da son jama’a. “Mutum ne da ba shi da kyamar mutane, ga kyauta. Idan aka ce lokacin azumi ne ko na sallah haka zai baibaiye mu da kyauta mu da ‘ya’yanmu. Allah ne kadai Ya san yawan mutanne da sarki ke kula da su a fadarsa. Shi ya sa a kowane lokaci idan aka tashi batun yawan ‘ya’yansa, ya kan ce shi kowa dansa ne. Kin ga a gidan nan duk da cewa mu yaran gida ne amma shi da ‘ya’yansa da matansa ba su wulakanta mu, muna gudanar da rayuwarmu mu da ‘ya’yanmu yadda muke so  ba tare da takura ba.” Inji ta.
 Sarkin Kano wanda shi ne Sarki na 13 a jerin sarautar Fulani ya dare karagar mulkin Kano ne a shekarar 1963 a lokacin yana matsayin ambasada a kasar Senegal, kawanaki kadan da rasuwar Kawunsa Sarkin Kano Muhamamd Inuwa wanda ya mulki Kano tsawon watanni bakwai bayan Sarki Sunusi ya yi murabus.  
An gudanar da shagulgulan bikim cikarsa shekaru hamsin a  bisa karagar mulkin Kano da bikin cikar sarkin shekaru 83 da haihuwa.
Bukukuwan wanda aka fara da gabatar da addu’oi na musamman a ranar Juma’a da kuma  liyafar cin abincin dare wacce aka gudanar a gidan gwamnati sai kuma hawan daba na musamamn da aka gudanar a fadar Sarkin a ranar Asabar ya samu halaratar dimbin jama’a ciki da wajen kasar nan.
A bangaren ‘ya’yan sarki mata su ma aba a bar su a baya ba wajen shirya bukukuwa na musamman don nuna tasu murnar ga mahaifin nasu. Tun a safiyar ranar Alhamis suka fara da gudanar da addu’o’in nuna godiya ga Allah wanda aka yi a Masallacin Shaikh Ahmad Tijjani da ke kofar Mata. A yammacin ranar kuma suka gudanar da walima a fadar sarki. A washegarin Juma’a kuma suka gudanar da saukar karatun Alkur’ani Mai girma inda aka gayyato yara ‘yan makarantun Islamiyya daban-daaban a fadin jihar don nema wa sarkin karin lafiya a wajen Allah (SWT).
Hajiya Maryam Bayeo  ta ce sun gayyato yaran ne don su gudanar da karatuttuka don neman dorewar lafiya ga sarkin, a matsayinsa na uba a gare su. “Kasancewar kowa ya san Mai martaba a kullum shi ke kan gaba wajen taimaka wa makarantun Islamiyya a jihar nan ya sa lokacin da muka mika gayyatarmu ga irin wadanann makarantu ba mu samu matsala ba, inda cikin murna malamai suka turo mana yaran makarantun don taya ubansu Sarkin Kano murnar cika Shekara 50 a bisa karagar mulki. Fatanmu shi ne Allah Ya kara wa sarki lafiya). Inji ta.
A lokacin da aka gudanar da hawan dabar Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero  ya nemi afuwar duk wanda ya saba masa a rayuwarsa, musamamn ma a tsakanin wadannan shekaru 50. Sannan ya bayyana afuwarsa ga wadanda suka yi masa laifi. Haka kuma ya nemi jama’a da su zauna da juna lafiya.
Shi ma a nasa jawabin, Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Namadi Sambo wanda ya wakilci Shugaban kasa Goodluck Jonathan a wajen taron, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi na’am da irin salon mulkin Sarkin Kano Ado Bayero wanda ta nemi sauran sarakunan da ke kasar nan da su yi koyi da shi.   
Da yake jawabi, Mai alfarma Sarkin Musulmi Alahji Sa’ad Abubakar 111 ya yi addu’ar Alalh Ya kawo zaman lafiya a garuruwan da aka sanya dokar ta-baci a kasar nan.
A nasa jawabin, Gwamnan jihar  Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana Sarkin Kano a matsayin wata babbar Katanga ce ga jihar, inda ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Sarkin tsawon kwana don Kano ta ci gaba da cin moriyar  irin salon shugabancinsa wanda ya ce abin koyi ne ga na baya.
Manyan  mutanen da suka halarcin bikin sun hada da Mataimakin Shugaban kasa, Alahaji Namadi Sambo da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Janar Muhamamd Buhari da Gwamnan Jihar Nassarawa Alhaji Tanko Almakura da sauran manyan mutane.