Cike gibin karancin gidaje a Najeriya

Kasancewar akwai kiyasin gibin gidaje miliyan 18 na iyali mai mutum shida, wannan wani tabbaci ne na cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 108 suna zaune ne a kuntatacce ko gida marar kyau.Wannan adadi da aka samo daga kididdigar Bankin Duniya ya tabbatar da cewa kashi 60 cikin 100 na ’yan Najeriya da ake kiyasin sun […]

Cike gibin karancin gidaje a Najeriya
Cike gibin karancin gidaje a Najeriya

Kasancewar akwai kiyasin gibin gidaje miliyan 18 na iyali mai mutum shida, wannan wani tabbaci ne na cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 108 suna zaune ne a kuntatacce ko gida marar kyau.
Wannan adadi da aka samo daga kididdigar Bankin Duniya ya tabbatar da cewa kashi 60 cikin 100 na ’yan Najeriya da ake kiyasin sun kai miliyan 180 suna fama da matsalar rashin gida. Abin da hakan yake nuni, shi ne kusan kashi biyu cikin uku na ’yan Najeriya suna rayuwa a muhallin da bai dace da tsarin kiwon lafiya ba. Bilhasali ma an kiyasta cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 20 suna zaune ne a gidajen da ko rufi ba su da shi.
Yayin da wannan kididdigar ke da ban tsoro kuma ta zamo sabuwar aba, tafiyar haiwaniyar da ake samu wajen bunkasa alkaryun kasar nan da karuwar jama’ar da ke sa kwarara zuwa birane tare da rayuwa a muhallan da aka gina da kayan gini marasa kyau kamar karan masara da ciyayin da aka samo daga gonaki da kwalaye da robobi ko kwana a kasan gadoji da gidajen da ba a kammala ba ko a kusa da bola, duk suna tabbatar da sahihancin wannan kididdiga da kuma matsalar rashin wadatar gidaje a Najeriya.  
Kuma baya ga kasancewar hakan manuniya ce ta rashin ci gaban kasa, yanayin yana jawo babbar matsala ga kasar nan tare da kawo cikas ga samar da ingantaccen tsarin rayuwa ga ’yan Najeriya a yanzu da kuma nan gaba. Kuma a yayin da ake sa ran jama’ar kasar nan su kai miliyan 260 nan da shekarar 2050 – shekara 35 nan gaba, matsalar karancin gidaje zuwa lokacin za ta dada zama barazana.
Duk da haka za a iya cike gibin idan aka magance matsalolin da suka shafi bangaren ta hanyar daukar matakai masu karfi a yanzu. Wasu daga cikin wadannan matakai shugabar Kamfanin Archibuilt Debelopment Serbices Limited, da kamfaninta ke shirya bikin nunin samfurin gidaje a shekara-shekara Misis Mobolaji Adeniyi, ta gano su, tare da bayyana su da karancin kudi da dokoki masu tsauri da ake fuskanta.
Lokacin da take magana da manema labarai a wajen nunin gine-ginen nan bana a Abuja, ta ce, rashin samar da rancen gina gidaje na dogon lokaci da tsattsaurar dokar amfani da fili na daga cikin matsalolin da suke dakile bunkasa samar da gidaje ga ’yan Najeriya. Kuma a yayin da hujjar da shugabar kamfanin na Archibuilt ke iya nuna matsalar bangaren kasuwanci, matakan da gwamnatoci da dama a dukkan fallaye ke dauka ba su taimaka wa lamarin ba. Fahimtar samun gida a matsayin ’yanci ne na ’yan kasa ke haifar da samar da canji a dimokuradiyyance wajen magance matsalar samar da wadatattun gidaje ga ’yan kasa.
Yanayin Najeriya gwamnatoci da dama kan kasa sauke nauyin da ke kansu na samar da muhallin da ya dace ga kowane dan kasa don ya rayu a cikin gidan da yake da rufi mai kyau a cikin walwala. Maimakon haka sai gidaje suka zamo abubuwa mafiya tsada kuma harka ta kudancewa a dare daya ta yadda masu kudi ne kawai ke amfana da su.
Misali kan haka, shi ne kokawar da tsohuwar Ministar Gidaje da Muhalli, Misis Amal Pepple  ta yi kan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen sauke nauyin da ke kanta game da kalubalen samar da gidaje da take fuskanta. A lokacin da take kaddamar da sababbin shugabannin hukumar gudanarwar Hukumar Gidaje ta kasa (FHA), ta koka kan gazawar hukumar na sauke nauyin da ke kanta na samar da gidaje ga al’umma.
A matsayinta ta hukuma ta gwamnati da aka dora wa alhakin tsara yadda za a bukansa samar da gidaje ga jama’a, gazawarta na nuna gazawar gwamnati a wannan bangare. Laifin ba na Hukumar Gidaje ta kasa ba ce kadai, rashin himmar gwamnati yana bayyana a kan yadda ake gudanar da Bankin Bayar da Rancen Gina Gidaje na Najeriya (FMBN) wanda yake zaune kasake a kan dukiyar da ake cirewa daga albashin ma’aikatan Najeriya a karkashin Asusun Samar da Gidaje na kasa  (NHF).
Bankin Duniya ya yi kiyasin cewa idan ana so a cike gibin samar da gidaje a Najeriya ana bukatar Naira tiriliyan 60. Idan kuwa haka ne a akwai bukatar gwamnati ta farka wajen sake mayar da kasar nan kan turbar da ta dace wajen fitar da tsarin samar da gidaje ga dukkan ’yan Najeriya cikin wani kayyadajjen lokaci a matsayin abin da take son cimmawa. Wannan manufa tana bukatar bunkasa samar da wasu tsare-tsare na samar da gidaje a dukkan sassan kasar nan, tare da amincewa da daidaitattun dokokin yin gine-gine da suke magana kan kayan gini da tsarinsa.
Idan aka yi tsari mai kyau, shirin samar da gidaje ga daukacin ’yan Najeriya zai dauki wani sabon salon a samar da kudi mai yawa da zai bunkasa tattalin arziki tare da samar da ayyukan yi da inganta rayuwa da jin dadin kowa da kowa.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50