Ciki da Gaskiya wuka ba ta huda shi
Hankalin talakawan Najeriya ya dugunzuma ainun, a makon jiya, sa’ilin da Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yomi Osinbajo ya bayyana masu cewa a yanzu haka akwai wasu fitattu, kuma hamshakan ‘yan Najeriya da suka sanya Shugaba Muhammadu Buhari a gaba, suna kokarin tadiye shi, ko kuma a ce lallashinsa don ya sassauta yaki da rashawa da […]
Hankalin talakawan Najeriya ya dugunzuma ainun, a makon jiya, sa’ilin da Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yomi Osinbajo ya bayyana masu cewa a yanzu haka akwai wasu fitattu, kuma hamshakan ‘yan Najeriya da suka sanya Shugaba Muhammadu Buhari a gaba, suna kokarin tadiye shi, ko kuma a ce lallashinsa don ya sassauta yaki da rashawa da ha’inci da rashin aminci da kuma yadda yake zargo azzaluman da suka zarme cikin wadanan miyagun dabi’un don tserar da kasar daga illolin da suka haddasa.
Wannan ba labari ne mai dadin ji ba, musamman ma ganin cewa dangane da haka ne talaka ya mika wa jam’iyyar APC da dan takaranta Muhammadu Buhari kuri’arsa a ranar 31 ga watan Maris don ya tabbatar an kai ga samun canjin da ya dade yana bukata wanda zai sanya shi shakar iskar ‘yanci, shi ya hole, ya more gardin rayuwa yadda ya kamata, a kasar da ba shi da wata sai ita, wacce kuma ita ce gatansa, gaba da baya.
Dagewa kan wacccan manufar da Shugaba Buhari ke bi yanzu haka, gadan-gadan don cika alkawarin da ya dauka na daga cikin daftarin manufofin jam’iyyar guda 10 don yakin neman zaben da ya gabata wadanda suka hada da kirkiro hukumomin ‘yan sandan jihohi da bayar da ilmi kyauta a dukkan matakan koyarwa da kuma yaki da rashawa ba sani, ba sabo.
Akwai kuma batun samar da guraben aiki guda 20,000 a kowace jiha da farfado da aikin gona da inganta dabarun samar da gidaje da kyakkyawan dabarun tsaron kasa da kare lafiyar jama’a. Sauran sune rarraba wa fakirai miliyan 25 Naira dubu biyar-biyar kowane wata don su tayar da komada da kuma bayar da alawus ga wadanda suka kammala yi wa kasa hidima.
Babu shakka wadannan kyawawan manufofi ne, ko kuma alkawura da suka sosa wa talakawa inda ke yi musu kaikayi, sun kuma shafa musu mai a baki ganin irin halin matsin da ake ciki, wanda ke sa mai kudi na kara kudancewa, matalauci kuma na kara talaucewa.
To, a yanzu haka dai gwamnatin jam’iyyar APC ta dukufa wajen yakI da rashawa domin haka ne kawai zai share mata fagen aiwatar da wadancan sauran alkawurran hankali kwance, musamman ma ganin cewa, a yanzu ita ce mai dakin da talakawa ke ciki, ta kuma fi kowa sanin inda yake yoyon ruwa da kuma dabarun yabewa.
Yakar rashawa, gaba-da-gaba,hali da dabi’a ce irin na jagorar gwamnatin APC, wanda bai sha’awar dulmuya hannayensa cikin baitul-malin talakawa, ba kamar na waccan gwamnatin ba da manyan jami’anta, wadanda ko gafiya ba ta kai su sata ba. Kasancewar Gwamnatin APC a karkashin adalin shugaba an samu shugabannin da ke sanya idanu kan na kasa da su a halin yanzu, wanda duk ya yi, ana yi masa, komai fadin ofishinsa da girman kujerarsa, kuma al’amura sun fara sauyawa.
Wadanda kuma suka zalunci talakawa, suka sassace dukiyarsu, sa’anan suka tumumushi wacce aka danka musu amana, sun fara shiga taitayinsu, domin kuwa ga su can ana ta yi masu terere, bayan dubunsu ta cika. Wasunsu sun guji shan kunya, sun yi wa kawunansu kiyamul-laili, sun fara maido da dukiyar da suka jida daga baitul-mali, bakinsu kanin kafarsu, wasu kuma sun ja daga, suna ta tujara, suna son gwada hali irin na gafiyar da ke son tsira da na bakinta. Wai kuma shi ne har wasu za su lalabo, su nemi a sassauta binciken, domin watakila sun hango cewa, za a rutsa da nasu, don sun tabbatar yana da hannu dumu-dumu cikin dukiyar da aka yi wawasonta, aka yi watanda da ita, suka kuma karbi rabonsu. Daga cikin irin kudin da aka rarraba wa hamshakan ‘yan siyasa har da wadanda aka ce an fitar don sun sunna wa malaman da suka yi addu’a don zarcewar azzalumai bisa mulki, kuma daga cikin wadanda suka fara wage baki don neman a yi sassaucin bincike har da malaman addini. Kai ka ji wani sabon salo, wai kiran sallah da usur.
Yanayin matsalolin kasar nan dai ba sabon abu ba ne ga gwamnatin Shugaba Buhari, tana sane da cewa rashawa ce dai ta kai kasar ga tsumburewa,ga shi nan kuma tana tsara hanyoyi da dabarun magance su, a kawar da su dungurungum, Najeriya ta komo sabuwa, ba ruwanta da fitintinun zamani. Ta ce ba gudu, ba ja da baya game da yaki da rashawa da kuma zargo azzaluman da suka dulmuya cikinta, daidai da yadda talakawan Najeriya ke so, suke kuma yaba mata saboda yadda ta tari aradu da ka, duk kuwa da cewa azzaluman na nan suna kokarin ramuwar gayyar da ba zu yi nasara ba.Talakawa dai na murna sun samu gwamnati mai sauraron kukansu, wacce take share masu hawaye da kuma agaza masu ficewa daga ukubar shugabanni marasa tsoron Allah, kuma masu tsananin son-kai. Ai kowace al’umma takan samu warki ne daidai kugunta, watau shugabannin da ke da hali da ra’ayi irin na mutanensu. A yanzu talakawa sun ga haza, sun gamu da sakamakon goyon bayan da suka ba gwamnatin azzalumai ta Googluck Jonathan, suna kuma ganin sauki da maslaha daga gwamnatin da suka zaba bayan sun yi nadama, sun kuma daura aniyar canja dabi’u da munanan halayen da suka kai su, suka baro a banza.
Manufofin jam’iyyar APC dai suna burge talakawa, kuma shugabanninta na yin tsayuwa, irin ta mai daka wajen aiwatar da su don amfaninsu da biyan bukatunsu, ba tare da biye wa mayaudara da mahassadan da ba su kaunar ganin ta kai kasar gaci.Wannan ne dalilin da ya sa ta dage wajen aiwatar da abin da talakawa ke sha’awa, watau murkushe zalunci da tsayar da adalci, kowa ya yi a yi masa. Abubuwan kirki da na alheri ba su samuwa cikin saukI, kuma jam’iyyar APC da shugabanninta sun san da haka, to idan har jama’a za su ci gaba da ba su gudummawar da ta kamata, za a yi maganin azzalumai ko da kuwa dukkansu za su taru su yake su, ba su yi galaba ba. A dade ana yi sai gaskiya, kuma shi ciki da gaskiya ai wuka ba ta huda shi.