Ciki ya yi batar-dabo a lokacin nakuda
Masu iya magana suna cewa, “abin mamaki ba ya karewa.” Wata matar wani dan kasuwa Sharif Ghazzali, da ke unguwar Daneji a cikin birnin Kano,mai suna Khajida Muhammad ce aka wayi gari cikin da take dauke da shi tsawon watanni har goma ya bata a daidai lokacin da ta ji alamar nakuda, kuma an je […]

Masu iya magana suna cewa, “abin mamaki ba ya karewa.” Wata matar wani dan kasuwa Sharif Ghazzali, da ke unguwar Daneji a cikin birnin Kano,mai suna Khajida Muhammad ce aka wayi gari cikin da take dauke da shi tsawon watanni har goma ya bata a daidai lokacin da ta ji alamar nakuda, kuma an je an yi gwajin ciki na likita har sau biyu amma ba a ga komai a cikin nata ba.
Sharif mijin Khadija ne ya shaida wa Aminiya haka a tattaunawarsa da wakilinmu.
Sharif Ghazzali ya tabbatar da cewa, tun a watan azumin bara ne aka daura musu aure da Khadija, ‘yar shekara 20, shi kuma yana da shekara 38 a yanzu, kuma har matar kaninsa da ya yi aure daga bayansa ta haihu, da kuma matar wansa duk sun haihu, amma matarsa Khadija ce ba ta haihu ba. ‘Ganin haka sai na shiga damuwa, ina cewa ko mene ne dalilin wannan jinkiri?”
Ya bayyana cewa, Khadija ce matarsa ta fari, kuma da shi da ita duk ba su taba haihuwa ba. Kuma ya ce irin haka bai taba faruwa a danginsu ba, sai dai a kan wata yayarsu wacce aka taba auna cikinta mai dauke da ‘yan tagwaye, amma aka ce mata jaririn ba shi da kai, sai kuma ta haife yaran biyu lafiya kalau kuma duk suna da kawuna.
Mutumin, wanda ya nuna wa wakilinmu takardun ganin likta na matar tasa da katin asibitin mai lamba 7385, ya nuna cewa, ta fara zuwa asibitin haihuwa na Sabo Bakin Zuwo ne da ke a Jakara, a karamar hukumar Birnin Kano da kewaye a ranar 28 ga watan Janairun na wannan shekarar da muke ciki, sannan kuma likita ya rubuta ranar 14 ga watan Mayun da ya gabata a matsayin ranar da ake sa ran za ta haihu, amma ba ta haihun ba.
Ita kuwa Khadija shaida wa wakilinmuta yi cewa, a cikin watan Yunin da ya gabata ne, a wata rana sai ta fara jin cikinta yana ciwo, ta zaci ma ko nakuda ce, “sai muka je wani karamin asibiti na Daneji, da likitar ta duba ni sai ta ce ba ta ga ciki tare da ni ba. Sai kuma ta tura ni wani wajen gwajin ciki na kudi, mai suna “Cibiyar Gwajin Ciki Ta Aisha”, na biya aka auna ni a ranar 17 ga watan Yun,i amma ba a ga komai ba, bayan da har fitsarina aka gwada.”
Ta ce daga nan ma ba su hakura ba, sai aka kai ta babban asibitin kwararru na Murtala da ke cikin birni, a ranar 19 ga watan na Yuni, inda nan ma sakamakon ya nuna cewa babu komai a cikinta. Haka nan kuma bayanin likita a jikin katin ya nuna cewa, “mahaifa tana lafiya sumul kuma girmanta daidai wa daida, sannan kuma babu komai a cikinta.”
Khadija kuma ta ce a watannin baya ta rika jin motsi a cikin cikin nata, amma yanzu kuma sai dai ciwo take ji a wani lokaci, kuma har yanzu yana nan da girmansa kamar dai akwai wani abu a ciki.

Mijin na Khadija kuma ya ce da farko abin ya tsorata shi, musamman ma lokacin da matar tasa ta mika masa katin asibiti ta shaida masa cewa an je an auna ba a ga komai a cikin nata ba. Ya ce sai daga baya ne kuma ya mayar da komai ga Allah. “ Da na ga haka babu wanda na fara fada wa sai wani Malam Muhammadu wanda yake yi mana limanci a unguwa. Sai ya ce mini irin haka ta taba faruwa da matar wani abokinsa, amma daga bisani kuma sai matar ta haihu, ya kuma ce a maida hankali wajen addu’a.”
Ya ce daga nan sai ya je ya tara malamai aka karanta littafin Ashafa, har aka sauke shi ,da nufin neman Ubangiji Ya warware wannan al’amari. Yana mai nuni da cewa har yanzu bai fid da rai matar tasa za ta haihu ba a cikin ikon Allah.
Haka kuma ya ce shi bai dauka ko aljanu ne suka yi tasiri a cikin matar tasa ba, sai dai ya ce tun farkon lokacin da ake jin ta dauki cikin ne da shi da ita suka rika yin mafarki da Manzon Allah (S.A.W.). Ya ce, “haka nan ma ta yi mafarki da Fadar Bege (mai wakar yabon Annabi wanda ya rasu) ta gan shi tare da Annabi, sanna ya ce mata, “muna sane da ke don ke tamu ce, kuma za ki haihu lafiya.”
A yayin da wakilinmu ya nemi jin ta bakin babban daraktan asibitin haihuwa na Sabo Bakin Zuwo, inda Khadija ta fara zuwa ganin likita, don tabbatar da cewa ko akwai ajiyayyun bayanai game da cikin nata, ya tarar daraktan ya tafi hutu mataimakiyarsa bat a nan saboda sun shiga yajin aiki.
Saidai kuma wani kwararren likitan mata da ke asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Dokta Zakari Muhammad ya bayyana wa wakilinmu cewa, al’amarin yana nuna cewa, “ta iya yiwuwa tun farko ma ba ciki ne da ita ba, sannan kuma duk da hakan za ta iya samun ciki a nan gaba ta haihu.”
Ya kara da cewa, koma dai meye, matsalar Khadija ba za a iya yanke magana daya ba, sai an duba ta a likitance tukuna.