Manyan Labarai• Created August 1, 2020 09:13
Cikin hotuna: Yadda aka yi Babbar Sallah a Najeriya
Ga wasu kayatattun hotunan ranar Babbar Sallah daga sassan Najeriya.
Ga wasu kayatattun hotunan ranar Babbar Sallah daga sassan Najeriya.
Masallata sun yi ruku’u a lokaci sallar idi a Maiduguri, Jihar Borno.Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar sallah, tare da ‘yan majalisarsa.Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya jagoranci iyalan gidansa sallar idi a gida.Gwamnan Borno, Babagana Zuluma tare da tsohon gwamna, Kashim Shettima a filin idi a Maiduguri.Yadda mata suka yi sahu gabanin a tayar da sallah a filin idi na Sultan Bello, Kaduna.Ministan fasahar sadarwa, Isa Ali Pantami yana gyaran kayan cikin ragon layya.Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II tare da iyalansa a ranar Sallah.Sahun maza a filin idi na Sultan Bello suna jiran isowar liman kafin a tayar da sallah.‘Yan kasuwa sun baje hajojinsu a kan titin da ke makwabtaka da filin idi na Sultan Bello.Shugaba Buhari da jami’an gwamnatinsa suna bin limamin Fadar Shugaban Kasa sallar Idi.Babban Limamin Ilori, Dakta Muhammad Bashir Imam-Soliu, yana gabatar da hudubar IdiMasallata na sauraron huduba daga Shaikh Muhammad Sulaiman bayan idar da sallah a filin idi na Sultan Bello.Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila a lokacin da zai yanka ragon layyarsa.Shugaba Buhari tare da iyalansa bayan saukowa daga idi a Fadar Shugaban Kasa.Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris filin idi na Kofar Doka, Zariya.