Cikin kowane mutum hudu na ’yan Najeriya daya na fama da hawan jini – Bincike
Wani bincike da Jami’ar Edinburgh ta kasar Scotland ta gudanar ya nuna cikin kowane mutum hudu na Najeriya daya na fuskantar hadarin ciwon hawan jini. Hawan jini yana daya daga cikin cututtukan da suke hallaka mutane ba tare da sun sani ba a Najeriya – kuma yana matukar karuwa sakamakon kwaikwayon rayuwar Turawa, kamar yadda […]
Wani bincike da Jami’ar Edinburgh ta kasar Scotland ta gudanar ya nuna cikin kowane mutum hudu na Najeriya daya na fuskantar hadarin ciwon hawan jini.
Hawan jini yana daya daga cikin cututtukan da suke hallaka mutane ba tare da sun sani ba a Najeriya – kuma yana matukar karuwa sakamakon kwaikwayon rayuwar Turawa, kamar yadda binciken ya gano.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Andrew Moffat ta ce masanan da suka gudanar da kididdigar kwakwaf don nazarin halin da jama’a ke ciki a Najeriya sun yi gargadin cewa wannan zai dada sukurkuta harkar kiwon lafiya da dama tangal-tangal take yi.
Masanan sun bukaci a kara wayar da kan jama’a da canja dabi’u da gwaji don gano cutar a matsayin babbar hanyar magance karuwar barazanar da cutar take yi ga jama’a.
Binciken ya nuna cewa hawan jini a Najeriya ya ninka na kasashen Afirka ta Gabas sau biyu, kuma kasa da kashi 20 cikin 100 ne kawai na ’yan Najeriya suka san suna da cutar.
Mutane masu fama da ciwon hawan jini suna fuskantar barazanar ciwon zuciya da ciwon hanta da shanyewar barayin jiki.
Masu binciken sun yi kiyasin akwai masu fama da ciwon hawan jini sama da miliyan 20 a Najeriya a shekarar 2010, inda yake shafar mutum daya a cikin mazaje uku da kuma mace daya daga cikin mata hudu. Kuma cutar za ta hauhawa zuwa miliyan 39 nan da shekara ta 2030.
Masana kimiyya a Jami’ar Edinburgh da suka gudanar da binciken sun ce gano cutar hawan jini a Najeriya da sauran kasashen Afirka na samun cikas ne saboda rashin adanannun bayanai kan masu fama da cutar.
An buga binciken nasu ne a mujallar yaki da cutar hawan jini Journal of Hypertension ta jami’ar. Kuma Dokta Dabies Adeloye, na Cibiyar Kimiyar Lafiyar Jama’a ta Jami’ar Edinburgh ya ce, “Mun gudanar da cikakken bincike mai inganci a sassan Najeriya kuma sun yin kiyasin ne kan karuwar yawan jama’a da suke harbuwa da cutar hawan jinin a kasar nan. Kuma muna fata wannan zai sa a bullo da tsare-tsaren da suka wajaba don fuskantar wannan matsala a banagren kiwon lafiya.”