Cikin shekara takwas ma’aurata sun ceci rayuwar tsuntsaye 200 a kasar Sin
A Lardin Sichuan da ke Kudu maso Yamacin kasar Sin, wadansu matasan ma’aurata sun ceci rayuwar tsuntsaye 200 da da suka ji rauni tun daga shekarar 2008, wadanda suka hada da nau’ukan ragon maza da gado da da mujiya.Ma’auratan Chen Kai da Zhang Li sunj dukufa da aikin ceton rayuwar tsuntsaye da kula da su […]
A Lardin Sichuan da ke Kudu maso Yamacin kasar Sin, wadansu matasan ma’aurata sun ceci rayuwar tsuntsaye 200 da da suka ji rauni tun daga shekarar 2008, wadanda suka hada da nau’ukan ragon maza da gado da da mujiya.
Ma’auratan Chen Kai da Zhang Li sunj dukufa da aikin ceton rayuwar tsuntsaye da kula da su a duk inda suka ga sun cikin tarko, sais u kwance su, su mayar da su daji da zarar sun warke. Bayan da suka ceci wasu tsiyoyi guda uku, sai daya daga cikin tsuntsayen ya zama abokin huldar su. Tsuntsun yakan kawo musu ziyara ya yi wasa sannan ya tafi.
Makwaftan wadannan ma’aurata na matukar sha’awar ziyarar gidan matasan don su ga kyakkyawan tsuntsun, wanda ake ganin tamkar gaisuwa yake kawo musu saboda kyautatawar da akla yi masa.