Cima-zaune ya auri mata biyu lokaci guda, zai tafi wata kasa neman aiki
Angon yana shirin tafiya kasar Malesiya don gwada sa’arsa wajen neman aiki.
Kafofin watsa labarai na kasar Indonesiya, sun wallafa wani labari mai ban al’ajabi na wani saurayi marar aikin yi da ya kammala shirin auren sabuwar budurwarsa da tsohuwar budurwarsa a lokaci guda.
Hakan na zuwa ne bayan an soke bikin aurensa da tsohuwar budurwar tasa tun da farko saboda rashin kudi.
- Budurwa ta kashe makwabciyarta ta hanyar daba mata wuka a Kano
- ’Yan bindiga sun sako daliban makarantar Bethel 15 a Kaduna
- Abin Da Ya Sa Hukumomi Suka Kasa Shawo Kan Kwalara
A karshen watan jiya ne, saurayin mai suna Korik Akbar mai shekara 20, daga Gundumar Lombok ta Tsakiya a Jihar Nusa Tenggara a Indonesiya, da yake cikin shirin auren sabuwar budurwarsa sai tsohuwar budurwarsa ta fashe da kuka tana neman ya aure ta a matsayin matarsa ta biyu.
Ta yi ikirarin cewa ba za ta iya hakura da shi ba.
Saurayin ya sanar da sabuwar budurwarsa mai suna Kotimah halin da ake ciki, inda ta gaya masa cewa, ta karbi tsohuwar budurwar a matsayin matarsa ta biyu.
Hakan ya sa Akbar ya amince ya aure su su biyun a biki daya, a lokaci guda.
“Tsohuwar budurwar mai suna Yuanita ta gano shirinmu na yin aure a kafafen sada zumunta, kamar yadda abokai da yawa suke taya mu murna. Saboda haka, ita ma ta nemi ta zama matarsa,” Kotimah ta bayyana wa manema labarai.
“Minti kadan bayan mun isa gidan Korik, ta bayyana cewa, ita ta nemi auren Akbar a matsayin matarsa ta biyu.”
Angon ya ce, ya yi mamakin ganin tsohuwar budurwar tasa, wadda suke tare tun shekarar 2016, amma bayan tattaunawa da iyalinsa, sai ya yanke shawarar auren su biyun.
Sun yi auren inda ya raba sadakin da zai ba matarsa ta farko ga su biyun.
“Ban yi tsammanin hakan zai faru ba, kuma na girgiza. Amma, lokacin da nake tattaunawa da dangina, na yanke shawarar auren dukkan ’yan matan biyu. Na raba sadakin da zan ba mata ta farko ga amaren biyun, wanda shi ne Rupiah miliyan 1.75 (daidai da Dalar Amurka 121), wato N49,789” inji angon.
Rahoton ma’auratan mai rikitarwa ya haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta na Indonesiya, kuma Korik Akbar da kansa ya gargadi samarin Indonesiya da kada su yi koyi da shi, domin zai yi musu wuya su rike mata biyu.
Angon yana shirin tafiya kasar Malesiya don gwada sa’arsa wajen neman aiki, inda zai bar matan biyu a gida.
Amare biyun sun ce, a shirye suke su yi aiki tare yayin da mijinsu ya bar gidan.
“Eh, dole ne mu kasance cikin shiri, me za mu iya yi?” daya daga cikin amaren Kotimah ta bayyana wa kafar labarai ta Kompas.