Cin amana ke yi wa sabuwar gwamnati tarnaki – danmasanin Jibiya
Wani tsohon dan majalisar dokoki a tsohuwar Jihar Kaduna da ya rike shugabancin kwamitin aiwatarwar majalisar a Jamhuriya ta Biyu, Alhaji Ashiru Aliyu Namarwa danmasanin Jibiya ya ce, cin amana da ha’inci da kuma son tara dukiya na daga cikin manyan dalilan da ke sa a samu sauyin gwamnati a siyasance. Alhaji Ashiru danmasani ya […]
Wani tsohon dan majalisar dokoki a tsohuwar Jihar Kaduna da ya rike shugabancin kwamitin aiwatarwar majalisar a Jamhuriya ta Biyu, Alhaji Ashiru Aliyu Namarwa danmasanin Jibiya ya ce, cin amana da ha’inci da kuma son tara dukiya na daga cikin manyan dalilan da ke sa a samu sauyin gwamnati a siyasance.
Alhaji Ashiru danmasani ya shaida wa wakilin Aminiya haka a wata hira da suka yi a Katsina ranar Asabar da ta gabata kan dalilan da ke kawo sauyin gwamnati tare kuma da yin adawa.
Tsohon dan majalisars ya ce, “Irin dambarwar da aka samu a wajen zaben shugabanni a lokacinmu ba a samu irin wannan ba, domin kuwa tun kafin a shiga majalisar mun san wanda za mu zaba.”
Ya ce ganin da wasu ke yi na sanya bakin jam’iyya mai mulki wajen zaben shugabannin ba katsalanda ba ne, “Dole ne jam’iyya ta sa baki domin duk wanda ya zo majalisar ya zo ne a karkashin jam’iyyar ne. Da yawa kafin ma ku ce za ku yi zaben sai kun samu wani horo na musamman ta hanyar laccoci daga wasu daga cikin iyayen jam’iyya da suka goge, inda za su yi muku bayanai akalla na tsawon kwana uku kuma jam’iyya ce ke yin wannan. Ke nan ashe komai sai da sa bakin jam’iyya,” inji shi.
Dangane da jan kafar da sabuwar gwamnati ke yi wajen nade-nade jami’anta, danmasanin ya ce, abin yana dogara ne da irin halin da ita sabuwar gwamnatin ta tsinci kanta a ciki. “Bayan cin amana da gwamnatin da ta bar gado ta yi, za a kuma tarar da an yi barna sosai, to, kuwa dole sai an tsaya an bi a hankali domin duk wanda za a ba wani mukami dole ne ya shiga ofis kuma ya fara aiki, to in babu kayan aiki yaya za a yi? Don haka masu fitowa yanzu suna surutai da sunan adawa shirme ne kawai suke yi saboda ana fara yi wa gwamnati adawa ne yayin da ta fara aiki, nan ne za a ga inda ta fuskanta,” inji Alhaji Ashiru.
Tsohon dan siyasar wanda ya ce, an fara samun lalacewar harkokin siyasa da mulki ne tun daga lokacin da aka ce mai shekara 25 yana iya rike karamar hukuma, ko mai satifiket din sakandire.
Sai ya sharwaci shugabannin da sauran ’yan siyasa cewa, komai za su yi su fara sa Allah a gaba ba tara dukiyar jama’a ba. Kuma ya bukaci ’yan boko su rika yin taka-tsantsan wajen gudanar da ayyukansu ta kula da dukiyar jama’a. Su kuma mabiya, su ci gaba da yi wa shugabanni kyakkyawar addu’a tare da ba su shawara tagari ba kokarin hada su da jama’a ta fuskar batanci domin neman fada ko maula ba.