Cin dankalin Turawa yana haifar da ciwon-suga – Bincike
Wasu masana kimiyya a kasar Amurka sun ce mata masu juna-biyu da ke yawan cin dankali za su fuskanci hadarin kamuwa da ciwon-suga ko diabetes.Masanan sun yi nazari ne a kan mata masu ciki dubu 21,000, kana suka fahimci cewa mata masu juna-biyu da ke cin dankali kwaya biyar ko fiye a mako na cikin […]
Wasu masana kimiyya a kasar Amurka sun ce mata masu juna-biyu da ke yawan cin dankali za su fuskanci hadarin kamuwa da ciwon-suga ko diabetes.
Masanan sun yi nazari ne a kan mata masu ciki dubu 21,000, kana suka fahimci cewa mata masu juna-biyu da ke cin dankali kwaya biyar ko fiye a mako na cikin hadarin kamuwa da ciwon-suga da kashi 50 bisa 100.
Sun bayyana cewa sitatin da ke cikin dankali na kara yawan suga a cikin jini.
A cewar masanan ciwon sugar mata masu juna biyu kan yi sauki bayan haihuwa, amma hadarinsa kan shafi iyaye mata da ta jariransu bayan wani lokaci mai tsawo.