Cin halal silar karbar addu’a
Daga Hudubar ASP Ibrahim Garba Azare Babban Limamin Masallacin Makarantar ’Yan sanda, Yelwa, Bauchi Godiya da taslimi:Bayan haka, ya ku bayin Allah! Hakika cin halal shi ne dalili ko sababin karbar kowace ibada, kamar yadda cin haram yake hana karbar kowace ibada. Saboda haka ne ma Allah Mai girma da daukaka Ya yi umarni da […]
Daga Hudubar ASP Ibrahim Garba Azare
Babban Limamin Masallacin Makarantar ’Yan sanda, Yelwa, Bauchi
Godiya da taslimi:
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Hakika cin halal shi ne dalili ko sababin karbar kowace ibada, kamar yadda cin haram yake hana karbar kowace ibada. Saboda haka ne ma Allah Mai girma da daukaka Ya yi umarni da cin halal a cikin wasu ayoyi biyu: Aya ta farko Allah Yana umartar ManzanninSa, ta biyu Yana umartar bayinSa muminai inda Ya ce: “Ya ku Manzanni! Ku ci daga halal, kuma ku yi aiki nagari.” sai fadinSa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ci daga tsarkakan abubuwan da Muka azurta ku da su, kuma ku gode wa Allah in kun kasance a gare Shi kuke bautawa.”
Allah Ya fara wannan umarni da cin halal kafin gabatar da ibada.
Kuma ya zo a cikin wani Hadisi daga Abu Huraira (RA) daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Allah Madaukaki, Tsarkakke ne, ba Ya karbar aiki sai mai tsarki. Kuma hakika Allah Ya umarci muminai da abin da Ya umarci Manzanni da shi. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku Manzanni! Ku ci daga halal, sannan ku yi aiki nagari. Lallai ne Ni Masani ne game da abin da kuke aikatawa.” Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ci daga tsarkakan abubuwan da Muka azurta ku da su…” Sai aka ambaci wani mutum mai doguwar tafiya ga shi ga ya yi kura, ga gizo (suma dukun-dukun), ya daga hannuwansa zuwa sama yana cewa: “Ya Ubangiji! Ya Ubangiji!! Alhali abincinsa haram ne, abin shansa haram ne, tufafin da ya sanya na haram ne, kuma guzurinsa haram ne da haram aka raine shi. To ta yaya za a karba masa addu’arsa?”
Haka ne hakika Allah ba Ya karbar addu’ar mai cin haram kamar sauran ibada, saboda haka ita addu’a ibada ce. Ya zo a cikin wani Hadisi daga Nu’uman dan Bashir (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Lallai halal a bayyane take, haram ma a bayyane take, sai dai a tsakaninsu akwai wasu abubuwa masu rikitarwa da mutane da yawa ba su sansu ba. To duk wanda ya ji tsoron aukawa cikin wadannan abubuwa masu rikitarwa hakika ya kubutar da addininsa da mutuncinsa. Kuma duk wanda ya auka a cikin wadannan al’amura, ya auka wa haram. Kamar dai makiyayin da yake kiwo a bakin iyaka, da kyar in dabbobinsa ba su fada ciki ba. Ku saurara! Kowane sarki yana da iyakarsa, ku saurara lallai iyakokin Ubangijinku su ne abubuwan da Ya haramta. Ku saurara a cikin kowane jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, to dukkan jiki zai gyaru, idan kuwa ta baci, to dukkan jiki ya baci. Ku saurara! Ita ce zuciya!” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Ku duba ya ku bayin Allah! Yaya mutane za su rika aukawa cikin abubuwan da Allah Ya haramta, suna cin dukiyoyin mutane da barna, kamar dai cinsu da shansu da tufafinsu da ababen hawansu da gidajensu da sauran harkokinsu, kai har ma da ibadarsu ta Hajji da Umara da sadaka da zakka da sauran ciyarwa da suke yi (da dukiyar haram ce). Alhali Annabi (SAW) ya ce: “Lallai Allah Madaukaki Tsarkakakke kuma ba Ya karbar wani aiki sai mai tsarki?”
Ya zo a cikin wani Hadisi daga dan Abbas (RA) ya ce: “An karanta mana wannan ayar a wurin Annabi (SAW) “Ya ku mutane! Ku ci daga abin da yake cikin kasa wanda yake halal kuma tsarkakakke.” Sai Sa’ad dan Abu Wakkas (RA) ya tashi ya ce: “Ya Manzon Allah (SAW)! Ka roka min Allah Ya sanya ni a cikin wadanda ake karbar addu’arsu.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Sa’ad! Ka kyautata neman abincinka (neman halal) za ka kasance a cikin wadanda ake amsa addu’o’insu.”
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ina rantsuwa da Wanda raina ke hannunSa, hakika da wani zai sanya loma daya ta haram a cikinsa, Allah ba zai karba masa addu’o’insa ba na tsawon kwana arba’in. Kuma duk mutumin da namansa ya ginu da haram ko riba, to wuta ce ta fi cancanta da shi.” Kuma ya zo a cikin wani Hadisi daga A’isha (RA) ta ce: “Abubakar Siddik (RA) ya kasance yana tare da wani yaro, sai ya fita tare da shi. Abubakar (RA) ya ci wani abu a fitar da ya yi, sai wata rana (yaron) ya zo da wani abu, sai Abubakar (RA) ya ci. Sai yaron ya ce masa: “Ka san mene ne wannan abin da ka ce?” Sai Abubakar (RA) ya ce: “Mene ne?” Sai yaron ya ce: “Ai na yi bokanci ne ga wani mutum a lokacin Jahiliyya, kuma ba ma na iya bokanci ba ne, sai dai kawai na kirkira ne. Shi ne da ya hadu da ni, sai ya biya ni ladana, to wannan shi ne abin da ka ci.” Sai Abubakar (RA) ya sanya hannunsa a cikin bakinsa har sai da ya amayar da abin da yake cikinsa. Kuma ya ce: “Da ya bar loma dayar nan a cikinsa, gara ya rasa ransa wajen kokarin fitar da ita.”
Huduba ta Biyu:
Ya ku bayin Allah! Hakika hanyoyin cin haram suna da yawa; daga cikinsu akwai: cin riba, kuma wannan muguwar dabi’a ta jefa mutane da yawa cikin halaka. Mutane suna cin riba ta dukkan nau’o’inta kamar Allah bai saukar da hani a kanta ba. Alhali Allah Madaukaki Yana cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku ci riba ninkin-ba-ninki, kuma ku ji tsoron Allah, lallai za ku samu babban rabo. Kuma ku ji tsoron wata wuta wadda aka yi tattalinta saboda kafirai. Kuma ku yi wa Allah biyayya kuma ku yi wa ManzonSa biyayya, lallai Allah zai yi muku rahama.”
Daga Annabi (SAW) ya ce: “Ku nisanci wasu abubuwa bakwai masu halakarwa. Sai suka ce: “Ya Manzon Allah! Wadanne abubuwa ne? Sai Annabi (SAW) ya ce: “Hada wani da Allah (shirka) da sihiri (tsafi) da kashe rai wadda Allah Ya haramta ba tare da hakki bad a cin riba da cin dukiyar maraya da gudu a fagen yaki da yi wa mace mumina, katangaggiya wadda ba ta san zina ba kazafi.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Ya Allah! Ka wadatar da mu da halal kuma Ka tsare mu daga haram.
Godiya ta tabbata ga Allah Shi kadai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a bisa Annabin da ba wani Annabi a bayansa.