Cin hanci a manyan hanyoyinmu: Wasika zuwa ga Shugaban kasa

Mai girma Shugaban kasa lallai na ji dadin irin amsar da ka bai wa Firayin Ministan Birtaniya cewa abin da ya fada kan cin hanci da rashawa ya yi wa Najeriya katutu gaskiya ne. Wannan ne ma musababbin rubuto maka wannan wasika tawa. Na farko in jinjina maka game da namjin kokarin da kake yi […]

Cin hanci a manyan hanyoyinmu: Wasika zuwa ga Shugaban kasa
Cin hanci a manyan hanyoyinmu: Wasika zuwa ga Shugaban kasa

Mai girma Shugaban kasa lallai na ji dadin irin amsar da ka bai wa Firayin Ministan Birtaniya cewa abin da ya fada kan cin hanci da rashawa ya yi wa Najeriya katutu gaskiya ne. Wannan ne ma musababbin rubuto maka wannan wasika tawa.
Na farko in jinjina maka game da namjin kokarin da kake yi na ganin an karbo dukiyar gwamnati da barayin gwamnati suka sace  suka azurta kansu tare da mayar da kusan kashi 90 na al’ummar kasar nan mabarata. Satarsu ce musababbin duk talaucin da muke ciki, asibitocinmu ba su aikin da ya kamata, saboda laifinsu. A lokacinsu, sai dai masu kudi su tafi waje neman magani, ilimi ya lalace saboda sun sace kudin sun giggina makarantu masu zaman kansu, sun wulakanta dan Adam wanda Allah (SWT) Ya karrama. Kowa na jinjina maka game da wannan namijin koaari da kake yi.
Dalili na biyu shi ne, in sake ankarar da kai a kan bala’in da ke faruwa a kan manyan titunan kasar nan,na cin hanci da rashawa da jami’an tsaro ke yi daga hannun direbobi. Ya Mai girma Shugaban kasa! Lokaci ya yi da za ka haska tocilarka ga wannan zalunci da abin kunya da jami’an tsaronmu ke aikatawa a hanyoyin kasar nan. An kusan daina bambance tsakanin ’yan fashi da makami masu tare matafiya su kwace musu kudadensu da jami’an tsaro masu gadin mutane da tsaron dukiyarsu. Daga Kano zuwa Legas, daga Katsina zuwa Fatakwal, ko daga Maiduguri zuwa Kano duk kanwar ja ce. Jami’an tsaro wadanda aikinsu ne su samar da tsaro a wadannan hanyoyi, su ne yanzu ke aikata abin da bai da bambanci da fashi da makami.
Wadannan azzalumai maciya amanar kasa, sun mayar da direbobin motocin haya kamar na’urar ATM. Ni ganau ne ba jiyau ba, na ga irin wadannan jami’an tsaro yadda suke tursasa wa direbobin haya cewa dole sai sun ba su kudi kafin a bar su su wuce. Kowane direba kan ba da daga Naira 200 zuwa Naira dubu daya, ya ta’allaka ga girman mota. Ma’ana direban babbar motar daukar kaya shi ne ya fi badawa da yawa, sai motocin safa ke bi musu. Wannan kudi da wadannan jami’an tsaro ke kwata daga direbobi, suna sanyawa ne kawai a aljifansu, sannan sukan yi kashe mu-ra-ba da shugabanninsu da ke turo su aikin.
Duk lokacin da aka samu direban da ya ki ba da irin wannan cin hanci, to sukan fasa masa gilashin mota, ko su huda masa taya ko su fasa madubin motarsa. Wani lokacin ma, har kisan mutane suke yi, idan sun nemi su ki ba da hadin kai.
Ya Mai girma Shugaban kasa, kowa ya san ka, kai mutum ne mai kamanta gaskiya, wanda a ka yi wa shaidar cewa bai son rashawa, kuma mutane na cike da fatan cewa ba za a samu irin wannan mummunan aiki na faruwa ba lokacinka, don haka don me tun hawanka, za ka bari wasu jami’an tsaron kasar nan su ci gaba da aikata abin da shi ne ka ki jini? Shin me ya sa ba mu taba jin ka yi magana a kan irin wannan nau’in cin hanci da rashawa da wasu jami’an tsaro ke aikatawa ba? Koko ba ka dauki irin wannan nau’in cin hanci da rashawa babban laifi ba ne? Ya Mai girma Shugaban kasa! Shirun da ka yi shi ya sa abin ke ci gaba da kazanta. Ya kamata ka fito fili balo-balo ka gaya wa shugabannin hukumomin tsaro na kasar nan cewa gwamnatinka ba za ta lamunci wannan aika-aika ba. Ya Shugaban kasa! A yau kasar nan idan tirela ta tashi daga Katsina zuwa Legas, direbanta kan kashe akalla Naira dubu 30, wajen ba da rashawa ga jami’an tsaro. Idan muka kiyasta a kullumi, direbobin tirela da na safa masu bin manyan hanyoyin kasar nan, suna asarar miliyoyin Naira ga rashawa. Wadannan kudade ne, ya kamata su taimaka wa direbobin su sauke nauyin iyalansu da na wadanda suka saya musu motocin.
Daga 1999 zuwa yau, Allah kadai Ya san ko direbobi nawa aka kashe saboda sun ki su ba da cin hanci ga jami’an tsaro. Wannan zalunci ya haddasa zanga-zanga da toshe manyan hanyoyi a lokuta da dama a sassa kasar nan, amma duk da haka hukumomi sun kasa dakile wannan zalunci.
Ci gaba da karbar rashawa daga direbobi da jami’an tsaro ke yi, na mayar da yaki da rashawar da gwamnatinka ke yi baya. Mutane game-gari na amfani da ire-iren wadannan nau’uka na rashawa wajen tantance baki dayan tasirin yaki da cin hanci da rashawar da kake jagoranta.
Ka sani ya Shugaban kasa! Wadannan jami’an tsaro masu karbar rashawa daga hannun direbobi, ba sa tare motocin manya, ba sa binciken motoci kamar marsandi ko fijo ko jif, domin suna gudun kada kilu ta ja bau.  Suna tare motocin haya ne kawai, inda suka san babu yadda talaka zai yi sai dai ya yi Allah Ya isa. Daga karshe ina son in bayyana maka jami’an da ke kan gaba wajen amsar rashawa daga direbobin motocin haya: Akwai Jami’an Road Safety (FRSC), akwai ’yan sanda da sojoji da jami’an kula da shige da fice (Immigration), wadannan su ne guma-guman.
Da fatan za mu ga canji ta nan bangaren.
Na gode
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka Ta kasa.  08165270879