Cin hanci: An yanke wa tsohon minista hukuncin kisa a China

Wata kotun Beijing a kasar China ta yanke hukuncin kisa ga tsohon Ministan Jiragen kasa na kasar Mista Liu Zhijun kan samunsa da laifin karbar cin hanci da amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba, kamar yadda kafar labarai ta gwamnatin kasar ta ruwaito a ranar Litinin da ta gabata, sai dai an mayar da […]

Cin hanci: An yanke wa tsohon minista hukuncin kisa a China

Liu Zhijun lokacin da ake yi masa shari’a a ChinaWata kotun Beijing a kasar China ta yanke hukuncin kisa ga tsohon Ministan Jiragen kasa na kasar Mista Liu Zhijun kan samunsa da laifin karbar cin hanci da amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba, kamar yadda kafar labarai ta gwamnatin kasar ta ruwaito a ranar Litinin da ta gabata, sai dai an mayar da hukuncin zuwa daurin rai da rai, inda akalla zai shafe shekara 10 a gidan maza.
An gabatar da Mista Liu ne a Kotun Al’umma ta Beijing ta Biyu a ranar 9 ga Yunin da ya gabata, kan cin hancin Fam miliyan shida (kimanin Naira biliyan daya da rabi) a cikin shekara 25 a tsakanin 1986 zuwa shekara ta 2011 da kuma yin amfani da mukaminsa wajen taimaka wa wasu mutum 11 su samu karin girma ko kwangila mai tsoka, inji kafar labarai ta dinhua. A watan Afrilun da ya shige ne aka zargi tsohon ministan a hukumance.
Kotun ta “Haramta masa shiga harkokin siyasa har abada tare da kwace dukkan dukiyar da ya mallaka,” inji kafar labaran.
Tsohon Ministan ya fashe da kuka bayan karanta masa hukuncin wanda aka dauki awa uku da rabi, kuma ya nemi afuwa kan yadda ya lalata nasararsa ta zamanantar da harkar sufurin jiragen kasa da cimma nasarar “mafarkin China,” kirarin da sabon shugaban kasar di Jinping yake amfani da shi.  
“Masu gabatar da kara sun ce Liu yana ya nuna halin kirki wajen amincewa da laifinsa da kuma nuna azama ta tuba,” inji kafar labaran.
Liu, dan wani manomi ne daga Lardin Hubei, inda ya fara aiki daga karamin ma’aikaci har ya zama minista a shekarar 2003, kuma shi ne kashin bayan zamanantar da harkar sufurin jiragen kasa na China, inda ya ba da kwangilar gina titin jirgin kasa mafi gudu mai tsawon mil dubu 10 kan Fam biliyan 170 da za a kammala a shekara ta 2020, a wani aikin injiniyoyi mafi tsada a tarihi a ’yan shekarun nan.