Cin hanci da rashawa ya haifar wa Tarayyar Turai asarar Dala biliyan 207 a shekara

Kwamishinar Harkokin Cikin Gida ta Tarayyar Turai, wadda ke da kasashe 28 a cikinta, ta bayyana yadda kungiyar ke yin asarar kudin Yuro biliyan 120 a kowace shekara, inda ta bukaci gwamantocin kasashen da ke cikin tarayyar da suk kara kaimi wajen shawo kan ayyukan cin hanci da rashawa.Kwamishina Cecilia Malmstroem, ta ce akwai yiwuwar […]

Cin hanci da rashawa ya haifar wa Tarayyar Turai asarar Dala biliyan 207 a shekara

Kwamishinar Harkokin Cikin Gida ta Tarayyar Turai, wadda ke da kasashe 28 a cikinta, ta bayyana yadda kungiyar ke yin asarar kudin Yuro biliyan 120 a kowace shekara, inda ta bukaci gwamantocin kasashen da ke cikin tarayyar da suk kara kaimi wajen shawo kan ayyukan cin hanci da rashawa.
Kwamishina Cecilia Malmstroem, ta ce akwai yiwuwar yawan kudin da tarayyar ke asara su haura abin da ta fada, duk da cewa kudin sun kai yawan kasafin kudin tarayyar, ko kuma kasafin daukacin kasashen da ke yankin, wanda zai gaza ne kawai da kashi daya cikin 100.
“Wannan kiyasin,”  cewar Malmstroem yana kunshe ne a cikin rahoto game da yankin, “ta yiwu adadin ya haura hakan.”
“Akwai fatan wannan rahoton ya cusa wa shugabannin siyasa karsashin dagewa a kowane matakin na gwamanti, don shawo kan ayyukan cin hanci da rashawa a daukacin fadin Turai,” inji ta.