Cin hanci ya durkusar da Nijeriya —ICPC

Hukumar ta yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance jajirtattu wajen fallasa ayyukan cin hanci da rashawa da kuma yaki da annobar.

Cin hanci ya durkusar da Nijeriya —ICPC

Hukumar Yaki da Rashawa (ICPC) ta ce cin hanci ya durkusar da Nijeriya tare da gurgunta cigaban tattalin arziki da zamantakewar kasar.

Hukumar ta yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance jajirtattu wajen fallasa ayyukan cin hanci da rashawa da kuma yaki da annobar.

“Cin hanci da rashawa ta durkusar da Najeriya, sun kawo koma-bayan tattalin arziki da na zamantakewa da siyasa. Idan ba mu kawo karshenta ba, tabbas zai kashe kasar nan,” in ji Kwamishinar Hukumar ICPC mai kula da shiyyar Jihar Bayelsa, Misis Ekere Usiere.

Ta bayyana muhimmancin tonon silili a matsayin muhimmin makamin yaki da rashawa, inda ta bukaci ’yan kasar da su kawar da tsoro su rika fallasa munanan ayyuka.

Usiere ta jaddada bukatar ’yan kasar cikin gaggawa wajen yakar matsalar, inda ta yi gargadin cewa rashin daukar matakin da ya dace na iya haifar da mummunan sakamako ga makomar kasar.

“Domin yaƙi da cin hanci da rashawa, idan kun ga wani abu, ku faɗa, idan kun ji wani abu, shi ma ku faɗa,” in ji ta.

Ta bayyana hakan a ranar Alhamis a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa domin bikin ranar yaki da cin hanci da sashin yaki da rashawa na hukumar NCDMB ta shirya.

Tun da farko, Babban Sakataren Hukumar NCDMB, Injiniya Felix Omotsola Ogbe ya jaddada kudirinsa na hana cin hanci da rashawa a cikin cibiyar tare da bayyana muhimmancin wayar da kan jama’a game da illolinsa musamman a tsakanin matasa.

DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa