Cin kayan marmarin da aka nika da sinadari na iya haifar da cutar Kansa – NAFDAC

Hukumar ta ce sinadarin na dauke da guba

Cin kayan marmarin da aka nika da sinadari na iya haifar da cutar Kansa – NAFDAC

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Mugunguna ta Kasa (NAFDAC) ta yi gargadin cewa masu cin kayan marmarin da aka nika su da sinadarin Calcium Carbide da cewa za su iya kamuwa da cututtuka kamar Kansa

A cewar hukumar, sinadarin, wanda galibi ’yan kasuwa ke amfani da shi wajen nikon, domin kayan su nuna da wuri, na dauke da guba.

Ko-odinetar hukumar a Jihar Bauchi, Josephine Abbas Daylim, ce ta yi wannan gargadi ranar Talata a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya na yankin Arewa maso Gabas.

Josephine ta ce an jima ana samun rahoton masu sanya gubar wajen nika danyen mangwaro ko ayaba da aka tsinko daga jikin bishiyarsa yana danye domin ya nuna da wuri, na da matukar illa.

Ta kuma koka kan yadda ta ce ana tallan magunguna a kwando a cikin rana, duk da cewa dama ba su da lasisi ko kwarewa wajen sayar da maganin a kan titi.

Sai dai jami’ar ta ce hukumar ba za ta iya shiga kowanne lungu da sako ba, dalili ke nan ma da shigo da jami’an tsaro da ’yan jarida domin su taya ta aikin.

Daga nan sai ta yi kira ga al’umma da su guji sayen irin wadannan kayayyakin domin su zauna lafiya.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan