Cin mutuncincin da ake yi wa PDP ya fi batuncin da aka ce tana yadawa -Farfesa Alkali
Farfesa Rufa’i Ahmad Alkali shi ne Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Jonathan a harkar siyasa, Aminiya ta nemi jin ta bakinsa a kan dalilinsu na murnan dage zabe da kuma siyasar batanci da ake zargin jam’iyyar PDP da yi ta kafofin yada labarai. Aminiya: Ana iya cewa hakarku ta cimma ruwa wajen ganin an […]

Farfesa Rufa’i Ahmad Alkali shi ne Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Jonathan a harkar siyasa, Aminiya ta nemi jin ta bakinsa a kan dalilinsu na murnan dage zabe da kuma siyasar batanci da ake zargin jam’iyyar PDP da yi ta kafofin yada labarai.
Aminiya: Ana iya cewa hakarku ta cimma ruwa wajen ganin an dage zabe?
Ahmad Alkali: wannan ba haka ba ne, lallai hukumar zabe ta ayyana 14 da kuma 28 ga watan nan a matsayin ranakun zabe, sai dai a karshe ya bayyana karara cewa hukumar zaben nan ba ta shirya ba, wannan shi ne babban dalili na dage wannan zabe a fahimtana. Saboda zabe yana da sharuda da dokoki wanda sai an cikabsu kafin a yi. daya daga cikinnsu mafi muhimmanci shi ne katin zabe, wanda kuma har zancen nan da muke yi a yanzu jama’a da dama ba su kai ga karbar katinsu ba. Saboda idan kana da wadanda suka yi rajista miliyan 68 amma ya kasance akwai wajen mutane sama da miliyan 20 da ba su karbi katinsu na zabe ba, alhali lokaci ya gabato, ka ga akwai nakasu a zaben, ko da an aiwatar da shi. Wannan katin na dindindin ke nan, ina ga katin da ake amfani da shi wajen kada kuri’an, samar da wadatattun malaman zabe, ba su horo da kuma aikewa da su wuraren da za su yi aiki, duk wadan nan abubuwa ne da sai an yi la’akari da su. Sannan ga matsalar tsaro, musamman a yankunan jihohin Arewa maso gabas din nan, dole a dubi tabbacin lafiyar ma’akatan zaben nan da na masu yin zaben, to wadannan da sauran abubuwa su ne suka hadu suka yi wa hukumar nan dabaibayi da ala tilas dole sai an dage zabe. Sai dai shi dan siyasa duk abin da ka yi sai ya nemi abin da zai ce, komi irin dalilai da aka bayar sai ya nemi ta cewa, bangarensa kawai zai duba ba ruwansa da na wadansu.
Aminiya: Sai dai a bayaninta hukumar zabe ta ce matsalar tsaro da aka bayar shi ne dalilin dage zaben nan, jama’a na zargin jam’iyya mai mulki da amfani da kusancinta da hafsoshin tsaro wajen cimman wannan buri.
Ahmad Alkali: Wannan ba gaskiya ba ne, kana jin hukumar zabe za ta ce duk da wadannan nakasu a bangarenta za ta iya aiwatar da karbabben zabe idan ba don an daga ba? ya kamata a rika yi wa jama’a adalci. Shi dai dan siyasa bai rabuwa da koraf,i duk wani dalili da a ka bayar ba za su yarda ba idan bai shafe su kai tsaye ba. Alal misali, idan a ce wannan matsala na raba kati ya shafi jihohi irinsu Legas ko Sakkwato ko Borno, a ce mutane kamar miliyan daya ba su yi zabe ba, su ‘yan hamayya za su yarda a yi zabe haka nan? Gaggawar me suke yi? Shekarar zaben da ya gabata ai a watan Afirilu aka yi zabe kuma an yi shi lafiya, har aka mika mulki a kan lokaci, me ya sa a yanzu za su ce ba haka ba ne, duk da matsalolin da aka lisafto? Dokar kasa ce ta bada damar wannan sauyi idan bukata ta taso, a saboda haka ba adalci ba ne a zargi jam’iyya mai mulki, ko gwamnatin tarayya.
Aminiya: daya daga cikin hanyoyin yakin neman zabenku shi ne tallace-tallace da ake bayyana su a matsayin batanci da ya wuce makadi da rawa, a matsayinka na mai bai wa shugaban kasa shawara a harkar siyasa me za ka ce a kan wannan?
Ahmad Alkali: Sai dai bai dace ka dubi bangare guda ba, su ma ’yan hamayyan ya kamata ka dubi abin da suke yi da yake musgunarwa, kuma ya kamata a dubi mene ne dokokin kamfe, kuma mene ne kafofin yada labarai suka ce a kan wadannan? Sai dai abin da ba a magana a kai shi ne yadda ake cin zarafinmu a wadansu lokuta a yayin yakin neman zabe, wannan al’amari ya faru a jihohi kamar biyar, mun je Katsina an yi jifa, mun je Bauci an yi jifa, mu je Adamawa an yi jifa, wannan ya saba wa al’adunmu da aka sani na Arewa na girmama baki, bare a tawaga wadda shugaban kasa ke ciki, wanda duk inda ya je a bangaren kasar nan tamkar gida ne a gare shi. Ba daidai ba ne a rika sa yara suna wadannan abubuwa, kuma muna fata za a kiyaye, kamar yadda a kullum muke roko. kasar nan tana da girma, idan ka yi wa wani ba za ka ji dadi ba idan aka yi wa naka a wani yankin. Haka nan ba daidai ba ne a rika cire mana tutoci da hotuna, har kuma ana kona mana motoci.
Aminiya: Sai dai a na danganta wadann nan al’amura a matsayin matsalolinku na cikin gida a sakamakon irin yadda kuka aiwatar da zaben fidda gwani na gwamnan a mafi yawan jihohi.
Ahmad Alkali: Wannan ba gaskiya ba ne, bincikenmu bai nuna haka ba.
Aminiya: daya daga cikin gwamnoninku gwamnan Bauci ya yi bayani a hakan, inda ya danganta shi da rigima ta cikin gida.
Ahmad Alkali: Wannan maganarsa ce kuma ba zan so in yi tsokaci a kan siyasar Bauchi ba. Ba dai adalci ba ne ka ce za ka tallata naka, sannan ka ce wani ba zai tallata nasa ba, alhali ko taba sigari wanda kowa ya san matsayinta ga lafiya, ana tallatata kowa ya na gani, abin da ake yi bai da bambanci da yanayin mulki na soja, na rashin girmama ra’ayin da ya bambanta da naka, in ko haka ne, ai gara a zauna a kan tsarin sojan gaba daya.
Aminiya: dage wannan lokacin zabe ya faranta maku rai, a yayin da ‘yan hamayya kuma suka yi bakin ciki da shi, a iya cewa faduwa kuka hango, su kuma suka hango nasara?
Ahmad Rufa’i: Wannan ba gaskiya ba ne, ai ba jam’iyyarmu kadai ba ce ta yi marhabin da dage zaben, akwai jam’iyyu da dama, kuma su ma ’yan hamayyan ya kamata su bai wa zaman lafiya muhimmanci fiye da komai, yau idan aka yi zaben nan a haka, sannan rigingimu suka bijiro a bangaren hukumar INEC da kuma tsaro, don Allah ya za su ji?
Aminiya: A karshe wane irin kamfe ’yan Najeriya za su yi tsammani daga PDP a kwanakin da aka kara?
Ahmad Alk ali: Za mu ci gaba da bin hanyoyi da suka dace wajen tallata dan takaranmu ga al’umma, kuma muna fata abokan hamayyanmu su ma za su bi wannan ka’ida wajen kauce wa cin zarafi da kuma musguna wa jama’armu a yayin kamfen, don dorewar wannan dimokoradiyya da muke hankoro.
….Tana fakewa da addini ne don babu abin kirkin da ta yi -Solomon Dalung
Barista Solomon Dalung daya ne daga cikin ‘yan kungiyar dattawan Arewa kuma jigo a babbar jam’iyyar adawa ta APC. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa daga zaben da aka yi yaudara ce kawai. Kuma tun da aka kafa Nijeriya ba a taba kashe kiristoci ba kamar yadda aka yi a zamanin wannan gwamnati ta Goodluck Jonathan. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Hussaini Isah Daga Jos
Aminiya: Mene ne matsayin kungiyarku ta dattawan Arewa dangane da daga wannan zabe da aka yi?
Solomon Dalung: A matsayinmu na dattawan Arewa mun dauki wannan al’amari na daga wannan zabe kamar juyin mulki ne aka yi wa ‘yan Nijeriya. Domin tun da farko hukumar zabe ta sanya ranar zabe shekara guda da ta gabata babu wanda ya ce wani abu. Sannan ana saura kwanaki 6 a gudanar da wannan zabe, hukumar zabe ta fito ta fadi cewa ta kammala dukkan shirye-shiryenta kuma za ta gudanar da wannan zabe kamar yadda ta tsara. Amma sai hafsoshin rundunar sojan Nijeriya suka fitar da takarda dauke da sanya hanunsu wadda ta yi baraza ga rayuwar shugaban hukumar zabe Attahiru Jega da sauran ma’aikatansa da dukkan ‘yan Nijeriya. Suka ce ba za su iya kare rayukan kowa ba a ranar zaben. Wannan abu da suka yi kamar juyin mulki ne. Don haka a matsayinmu na dattawan Arewa ba mu karbi wannan abu da suka yi ba. Kuma muna kira kan su sauka daga kan matsayinsu domin sun yiwa kundin tsarin mulkin kasar nan zagon kasa. Bayan sun sauka kuma a kama su a hukunta su domin sun ci amanar kasa.
Aminiya: Kana ganin nan da makonnin 6 da jami’an tsaron na Nijeriya suka dauka cewa za su gama da ‘yan kungiyar Boko Haram zai yiwu?
Solomon Dalung: Wannan magana da suka kawo babu wani mai hankali da zai yarda da ita. An yi shekaru 6 ana yin wannan yaki amma ba su iya murkushe wadannan ‘yan Boko Haram ba. Sai dai ‘yan Boko Haram suna ta cin karensu ba babbaka, suna ta sace-sacen mata da kananan yara. Ya zuwa yanzu sun wwace yankuna da dama wanda ya kai kananan hukumomi 14 a jihohin Adamawa da Yobe da Borno, kuma sun kwace masarautu kamar guda 7 a wadannan yankuna, amma ba a iya yi musu komai ba. Sai a yanzu ne za a ce a cikin makonni 6 za a murkushe su. Wannan yaudara ce kawai, ana nema ne a shigar da siyasa a cikin al’amarin tsaro. Amma babu gaskiya a ciki kuma babu aniya kyakkyawa ta magance tabarbarewar tsaro a Nijeriya.
Aminiya: A tallace tallacen yakin neman zaben shugaban kasa Goodluck Jonathan da ake gabatar a kafofin watsa labaran kasar nan a halin yanzu, ana ta amfani da addini, me za ka ce kan wannan al’amari?
Solomon Dalung: Babu abin da shugaban kasa Jonathan zai nuna wa ‘yan Nijeriya, shi ya sa ya koma yana fakewa da addini. Duk mutumin da aka zaba idan yana son a sake zabensa, zai nuna wa mutane irin ayyukan da ya yi ne. Amma shi shugaba Jonathan bai yi aikin komai ba, sai aikin tsunduma kasar nan a cikin rikice-rikice. Domin a lokacin da ya karbi mulkin Nijeriya kasar tana dunkule, amma yanzu ‘yan Boko Haram sun mamaye wadansu yankuna suna mulki tare da shi.
A karkashin mulkin Jonathan ana satar kudaden jama’ar Nijeriya ba ji ba gani, a mulkinsa kowane babban mai mulki yana babakere da dukiyar kasa, a mulkinsa an sace ‘yan mata darurruwa wadanda har yanzu ba a dawo da su ba. Idan ka hada wadannan abubuwa da suke faruwa a mulkinsa za ka ga ba shi da abin da zai nuna wa ‘yan Nijeriya a matsayin aikin da ya yi. Sai dai ya nuna cewa ya gallaza wa ‘yan Nijeriya, don haka mutum mai irin wannan ba shi da abin da zai yi illa ya fake da addini yana cewa shi kirista ne a goyi bayansa.
Mu kiristoci a Nijeriya mun sani cewa a zamanin mulkin Goodluck Jonathan mun sha wahalar da ba mu taba sha ba a tarihin kasar nan. Ba a taba kashe kiristoci a Nijeriya ba kamar yadda aka kashe a wannann gwamnati ta Goodluck Jonathan, saboda haka ba shi da wata hujja da zai yi wata karya ya ce wai shi kirista ne. Kuma wannan abu da yake yi abu ne wanda akwai ranar da Allah zai tona asirinsa.
Aminiya: Mene ne kake ganin ya sanya wadansu suke ta kokarin ganin sun hana Janar Buhari wannan takarar shugaban kasa da yake yi?
Solomon Dalung: Saboda sun ga za a kayar da su ne, don haka suke nemansu yi wa damakoradiya karan-tsaye. Amma shi Janar Buhari ba yau ya fara tsayawa takara ba, domin ya tsaya zabe a shekara ta 2003 ya tsaya a shekara ta 2007 ya sake tsayawa a shekara ta 2011. Abin tambaya a nan shi ne, a dukkan wadannan zabubbuka da ya tsaya da wace takarda ya tsaya? A lokacin ai ya tafi kotu kan wadannan zabubbuka mene ne ya sanya a lokacin ba su kalubalance shi ba, ta hanyar cewa shi ma ba shi da takardar makaranta?
Saboda haka masu wannan kokari shure-shure ne suke yi wanda ba zai iya hana su mutuwa ba. Don haka daga lokacin zabe ba wai an daga masu zaben ne ba, masu zabe suna nan, don haka rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya.
Aminiya: To karshe wanne sako kake da shi zuwa ga al’ummar kasar nan?
Solomon Dalung: Sakon da nake da shi zuwa ga al’ummar Nijeriya shi ne kowa ya yi hakuri kuma a gudanar da komai a cikin kwanciyar hankali da lumana. Kodayake wannan juyin mulki da hafsoshin sojojin Nijeriya suka yi, sun so ne a tada rigima domin su samu hujja su ce ana rigima don haka sun karbi mulki. To wallahi wayo ya san na ki. Don haka mu yi hakuri mu cigaba da neman mutane ta hanyar yakin neman zabe, har Allah Ya kai mu wannan rana ta 28 ga watan Maris da suka sanya mu fito kwanmu da kwarkwatarmu a cikin lumana mu kori zalunci a kasar nan, a samu a kafa gwamnati mai aminci wadda za ta ja kasar nan zuwa ga cigaba.