Cin zarafin Annabi: Malaman Musulunci sun la’anci mujallar Charlie Hebdo
kungiyar Manyan Malaman Musulunci ta Duniya a karkashin jagorancin Sheikh Yusuf Al-karadawi ta la’anci mujallar zanen takala ta Cherlie Hebdo ta kasar Faransa bayan ta sake wallafa sabon zanen da ta danganta da Manzon Allah (SAW). Malaman sun ce wannan mataki ne da ke kokarin tunzura Musulmin duniya.A cikin wata doguwar sanarwa, Sheikh Yusuf al-karadawi, […]
kungiyar Manyan Malaman Musulunci ta Duniya a karkashin jagorancin Sheikh Yusuf Al-karadawi ta la’anci mujallar zanen takala ta Cherlie Hebdo ta kasar Faransa bayan ta sake wallafa sabon zanen da ta danganta da Manzon Allah (SAW).
Malaman sun ce wannan mataki ne da ke kokarin tunzura Musulmin duniya.
A cikin wata doguwar sanarwa, Sheikh Yusuf al-karadawi, ya ce babu wata hujja da wani zai yi zane ya dangata da Manzon Allah (SAW), tunda ya san Musulmi ba su son haka.
kungiyar ta kunshi masana Musulunci da suka fito daga akidun Sunni da Shi’a da sauran akidu.
Malaman sun ce wannan alamu ne da ke nuna kasashen Yammacin Turai suna kyamar Musulunci. Kuma matakin zai kara tunzura Musulmi musamman masu tsaurin ra’ayi.
Sheikh karadawi, mai shekara 88 babban malami ne a Masar, amma yanzu yana rayuwa ne a kasar katar bayan hambarar da gwamnatin Ikhwanul Muslimina ta Muhammed Morsi.
Haka ma Sheikh Ahmed al-Ghamedi ya ce sake wallafa zanen ganganci ne. Shiekh Ghamedi, ya ce ya wajaba duniya ta fahimci cewa Annabawa Manzannin Allah ne, don haka kuskure ne wani ya mayar da su abin wasa.
kasashen Musulmi da dama sun yi Allah wadai da mujallar Charlie cikinsu har da Iran da katar da Masar da Turkiya. Kuma dubban Musulmi kuma sun yi zanga-zanga a kasar Philipphines domin nuna adawa da mujallar.