Cin zarafin mata ya sa na kafa cibiyar Trustcare- Mbantira
Mbantira danladi Baido ita ce Shugabar Cibiyar Trustcare Foundation da ke Abuja, a hirarta da Aminiya ta bayyana dalilin da ya sa ta kafa cibiyarta da kuma matsalolin da take fuskanta. Aminiya: Mene ne ya ja hankalinki har kika kafa wannan cibiyar?Mbantira: Zan iya cewa na dade ina tausayin halin da mata suke ciki, amma […]
Mbantira danladi Baido ita ce Shugabar Cibiyar Trustcare Foundation da ke Abuja, a hirarta da Aminiya ta bayyana dalilin da ya sa ta kafa cibiyarta da kuma matsalolin da take fuskanta.
Aminiya: Mene ne ya ja hankalinki har kika kafa wannan cibiyar?
Mbantira: Zan iya cewa na dade ina tausayin halin da mata suke ciki, amma na yanke hukuncin in kafa cibiya a shekarar 2008 ne, saboda wani al’amarin ya taso wata rana na je wani biki da ya shafi mata, a wurin bikin ne aka ce matan da aka taba cin zarafinsu su fito, a dakin taron akwai mata kusan dubu daya, amma abin da ya ba ni mamaki sai na ga mata kusan dari tara sun fito. Kuma yawanci matan masu karancin shekaru ne, hakan ya sanya na fara tunanin yaya za a ce irin wadannan matan sun shiga irin wannan halin. Bayan na ji irin halin da suka shiga ne tun daga wurin taron har na je gida ina kuka. Yara kanana an yi musu fyade, wasu an yi musu ciki. Na samu maigida ya kuma ba ni hadin kai.
Aminiya: Bayan kin kafa wannan cibiyar wadanne ayyuka ne kika zabi gudanarwa?
Mbantira: A shekarar 1999 na je kasar Sifen, an hada mu da wani mutum dan Sakkawato da ke aiki a karkashin ofishin jakadancin Najeriya a kasar Sifen. Wata rana mun shirya za mu fita sai ya ce mana ba zai samu dama ba, saboda jakadan Najeriya a kasar ya dawo daga tafiya, sai muka ce masa yaya za mu yi ke nan? Sai ya tambaye mu wuraren da muke son zuwa a Madrid (babban birnin kasar), sai ya ce mu rubuta adireshin wurin da za muke son zuwa mu ba dan tasi din da muka samu, sai na ce masa yaya za mu ba dan tasi, sun iya karatu ne? Sai ya ce ai a nan kasar kowa ya iya karatu da rubutu, ilimi a kasar kyauta ne, gwamnati na daukar nauyin karatu. Daga farko dai ban yarda ba, amma bayan mun fita mun samu dan tasi, sai ya kai mu wurin da muka rubuta masa, sai ya zama mun daina tuntubar mutumin da aka hada mu da shi, ya kira mu, a nan na sanar da shi ai mun zama ’yan gari. Hakan ya sanya na yi tunanin duk macen da ta iya karatu to za ta iya yi wa kanta abubuwa da dama. Sai na zabi ilimin mata a matsayin abu na farko da nake so in samar. Abu na biyu kuma shi ne, mu koya musu sana’o’in hannu.
Aminiya: Daga kafa wannan cibiya mata nawa kuka koya wa sana’o’in hannu, nawa kuka biyawa kudin makaranta?
Mbantira: Na fara ne a Jihar Taraba saboda daga nan na fito, mun kaddamar da cibiyar a Taraba, inda na samu mata 100, bayan mun gudanar da bincike sosai, sai na gano mata 33 ne suka cancanci a taimaka musu, amma abin mamaki a cikinsu daya ce ta ce tana so ta koma makaranta, sauran sun ce sun fi son a koya musu sana’o’i kuma hakan muka yi. Na tambayi wata me take yi, sai ta ce mini tana sayar da kunun zaki, amma matsalarta ita ce, ba kullum take yi ba saboda aron kula take yi, wani lokaci kuma haya, sai muka ba ta jari, wadansu matan ma iyayensu sun kore su saboda sun yi ciki, inda suke zama da kakanninsu, ko ’yan uwansu, haka muka koya musu sana’o’in hannu. Wadansu mun koya musu yadda ake gyaran gashi, mun kuma ba su jarin sun bude wuraren da suke gyaran gashi. Wasu kuma muka koya musu yadda ake dinki. Bayan wata shida na koma wurinsu, inda suka ce mini rayuwarsu ta canza, kuma nima na ga hakan.
Aminiya: bangaren karatu fa?
Mbantira: A Taraba mace daya ce ta ce tana son makaranta, mun kuma dauki nauyin karatunta. Daga nan muka gano yawancin ’yan Taraba sun fi son a koya musu sana’o’in hannu, ko a ba su jari, sai muka rika ba su shawarwari cewa karatu ya fi muhimmanci. Amma nan gaba za mu je ko’ina a Najeriya. A yanzu ya kamata a ce muna Gusau, saboda abubuwan da suke faruwa sai muka dan dakata sai nan gaba. A nan Abuja akwai ’yan mata shida da muka dauki nauyin karatunsu.
Aminiya: Batun nasarori fa?
Mbantira: Nasarar da zan ce mun cimma ita ce ’yan mata 6 da suke karatu yanzu haka, saboda idan ka ilimantar da mace tamkar ka ilimantar da al’umma ne gaba daya, ka ga hakan ai nasara ce.
Aminiya: Wadanne kalubale kuke fuskanta?
Mbantira: kalubale na farko da muke fuskanta daga iyaye ne, saboda ba su fahimci muhimmancin ilimi ba, wani ya ce ba shi da kudi, tabbas iyaye za su iya kawai dai ba su damu ’ya’yansu su je makaranta ba ne. Wani lokaci za ka ji ana cewa komai ilimin mace ai aure za ta yi, tabbas za ta yi aure, amma idan tana da ilimi za ta fi iya zaman auren, sannan idan tana wani abu za ta taimaka a gidan aurenta. Ni ma da ban yi karatu ba, to ba zan yi tunanin taimaka wa mata ba. Su ma matan yanzu sun fi so a ba su kudi wato jari, ba su damu da karatu ba. Mun je Dei-Dei a nan Abuja duka matan sun ce kudi suke so. Na uku kuma ba a san mu, saboda idan an san mu mutane za su ba mu gudunmuwa, inda mu kuma sai mu taimaka wa mata da yawa.
Aminiya: Yaya kike ganin wannan cibiya a nan gaba?
Mbantira: Ina hasashen wannan cibiya za ta zama abar alfahari ba ma a Najeriya har a Afirka. Domin muna so mu samu ofis-ofis a dukkan jihohin Najeriya.
Aminiya: Wane kira kike da shi daga karshe?
Mbantira: Ina kira ga iyaye da mata cewa idan sun ji wani kira ba sai lallai daga cibiyarmu, to su saurari abin da cibiyar take tafe da shi. Na san cewa akwai cibiyoyi da ake ba su kudi amma ba sa yin abin da ya kamata, amma mu da kudinmu muke yi, sannan kofa a bude take ga duk wanda yake so ya kawo taimakonsa.