Cincirindon ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka
Cincirindon ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka Cincirindo ’Yan kwadago dodo-dodo Hargowa da harigido Tsibin kayan dadi a Kwando Wani abincin yai kama da bado Kamfanin Dalilin-taronsu Kun hadu da masu tafka musu Labarin kuliya da kusu Kowa ya diro a kansu Ban da shahasha da sususu Baffan Editoci Ya nuna karamci Muma kada mu yi […]
Cincirindon ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka
Cincirindo
’Yan kwadago dodo-dodo
Hargowa da harigido
Tsibin kayan dadi a Kwando
Wani abincin yai kama da bado
Kamfanin Dalilin-taronsu
Kun hadu da masu tafka musu
Labarin kuliya da kusu
Kowa ya diro a kansu
Ban da shahasha da sususu
Baffan Editoci
Ya nuna karamci
Muma kada mu yi butulci
Ko zantukan batanci
Sai mu dan yi kawaici
Zancen ba habaici
Masu jefa mu cikin kunci
Da ke nuna bambanci
Ina tai muku barkwanci
Har an dauke ni dillalin dolanci
Jita-jitar jakkanci
Sakatar subul da bakan sokwanci
Dabarbarun dabbanci
korafi da kulafuci
Tubulin tada ginin Turanci
Dokoki na bukatar kanikanci
Don kawar da jahilci
Sai a tabbatar da adalci
Kowa da kowa a samu kusanci
Sai mu kauce wa kaskanci
’Yan gada-gada
Sun yi kaka gida
Suna ta baragada
Sun gaza haura gada
Mu dai dare kan danda
A kiyayi far-far-da-ganda
Kar a kwada muku sanda
Farmaki miyagu har su saduda
Mu rage yawan kasada
A daina waskiya a fada
Ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka
Ciranin kaka
Cari da caccaka
Cizon cinnaka
Cankar kubu da caka
Gwarzon gwaraza
Gutsuri gwaza
Gafalallu sai an gwabza
Girrgiza-girrgiza
Gundumi ya gaza
A tabbatar da adala
A kawar da juhala
Doka na hana wahala
Mai laifi a tsala masa bulala
Sila ta fi salsala da salala
Ga karatu dalla-dalla
Watsatsaken kauce wa cin kwala
Wasu na ta cin alala
Sun samu salala
Sun bar mu muna lalalala
Wa’adin sallama
An samu makama
Malam da malama
An bi ku da lalama
Yanzu a nai muku takama
Kar ai mana cin duhu
An nunke mu a buhu
Nauyinmu huhun ma’ahu
Ba a saye taro da ahu
A daidaita sahu
kiren karairayi
Ciwonsu na da kaikaiyi
Ciniki babu tayi
A sai kayan yayi
A kauce wa dibar yayi
Masu mukami
Kun dau makami
Kuna yi mana bambami
Kar ku jefa jama’a zullumi
A karke da salallami
Fanco
Watsattsaken kan ga gilashi
Murguda bakin cin kilishi
Cikin harshen ingilishi
Kaico!
Gadin yana
Gudun magana
Garadan gidan zana
Gardamar masana
Gada-gadargarada na zayyana
Burgar bugun gadi
Banga-da-gadi
Bugar gardi
Baragada marar adadi
barambaramar kaidi
A kiyayi surutun ’yan baka
Otal din Ci-da-kanka
An nemi a kyautata ayyuka
Kiraye-kirayen shugabanni duka
Wasu sun ci kare ba babbaka
Kwankwatsa da tsattsagar ci-maka
dundume kururu da marka- marka
A dubi na-mujiyar hankaka
Mayar da dan wani naka
Zalunci ke haifar da kiki-kaka
Ja-gaban masu watsattsake
Wassafa tsarin damo-da-kura-diyya
Wasan Samson siya-siya
’Yan takara na take-take
Masu taka-kara na make-make
Malam Mahmudu
Yai awo a mudu
Siyasa an tafka rudu
Neman mukami har a Bungudu
Sun karade Arewa da Kudu
A rana ta karamin lauje da sili ga watan Ukun-toton-Baba mun halarci CINCIRRINDON CE-CE-KU-CEN CI-DA-KANKA, inda muka kwashi kwalamn da makwalashe, a wajen tande-tande da lashe-lashe, muka yi nashe-nashe. Kodayake dai da farin farawa Baffan Editocin kamfanin wallafa Amintattun jaridun kasar Haurobiya ya bijiro da batutuwa kan yadda za a inganta watsatttsaken rahotannin al’amuran da ke wakana a daukacin fadin Haurobiya. Sai kuma malam Mahmudu Ja-gaban masu watsattsake a jaridar Dalilin-taronsu, wanda ya nusar da mu yadda ake lalubo batutuwan masu wasan Samson siya-siya da kwakwalen talakawa don neman darewa bisa karagar mulki.
Su ma jiga-jigan jan ragamar ’yan kwadagon wannan kamfani sun bijiro da baturtuwansu, inda suka karke da mayar da martini korafe-korafen ’yan kwadagon kamfanin da ke ganin akwai NAdI A CIKIN LAUJE game da sababbin tsare-tsaren da aka fito da su, musammman kan wadanda ke hankoron RIRITA TAYA ko MURABUS daga fafutikar cin CUKUBUS da ALGARAGIS da ALKUBUS kafin su rrankaya birnin TAGADAS wajen CACUMAR masu CAMMMAR cin CA’AMMAS, don sauke nauyin kayan da aka jibga musu, inda suke ta artabu da KULIYA DA KUSU, wadanda ke kyarar baza labarin yadda suka bula ASUSU, suka mayar da al’ummar kasa taron SHASHASHA DA SUSUSU.
Batu na ingarrman karfen karafan titin tarragon layin dogo, mun yaba kokarin kamfanin wallafa Amintattun jaridu da mujallun kasar Haurobiya, illa dai kawai akwai ’yan ba ni na iya a jerin masu jan ragamar jigata ’yan kwadago da ke haifar da tarnaki a wajen CANAKAR KUBU- JA-DA-BAkA DA CAKA na GWARZON GWARAZA a wajen cin gwaza, shi ya sa aka yi musu gunji da GAZA. Lallai a daina wasan KARTA da rayuwar ’yan kwadago masu laluben kadago a daukacin lokutan wulwulawar AGOGO. A dai tausaya wa su GWAGGO. Kuma akwai ’yan dugwi-dugwi da ke gararamba a KANGO ja-gabansu shi ne GIZAGO, uhm! Giza-gizon dakin GWAGGO. Wasu na shirin samun gwaggwabar ladar kWADAGO. Idan kuwa ka ga na-mujiya kURU-kURU, to an samu masu SHARbAR SHAWARMAR SHIRRUWA SHIRU, da sun ci sun tande sais u bar kowa ya yi ZURU-ZURU.
Su kuwa ’yan makaranta masu koyon watsattsake da fallee shafukan mujallu da makalu a Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya sun yi DODO-DODO karkashin jagoran Malam DODO na farfajiyar DODORIDO, wanda ke fafutikar ganin an hana kWADO da darar HARIGIDO da rayuwar al’umma dungurugum. Don haka na yi ZUGUM zan yi GUM. Kada a bari ‘ya’yan innna da baba su yi DUKUM! Kunkumadi launin KUM-KUM!
Haurobiyawa a bi kA’IDA don samun FA’IDA, sannan a bi DOKA don kada kowa ya KOKA! Sai a kiyayi shaci-fadin ’yan BAKA rrani da KAKA!
Wannan shi ne Cincirindon ce-ce-ku-cen Ci-da-kanka da kamfanin wallafa jariodu da mujallu ya saba gudanarwa a kowace shekara, don kada a yi kakara a wajen taka-kara ko neman mukami a wajen takara. Mun dai samu sarrafa SAMFARERA daga ribar SAFARA, saura mu kwashi GAGARUMAR GARARUMAR GARA, in an kauce wa tsikarar na-mujiya a wajen gyaran GIRA, musamman in aka fatattaki masu tsuwurwurta ’YAN GYARE-GYARE IRIN NA GYARE DA KUREGE.
Da zarar an amsa kiran makaranta to za a daina YASAR TANKIN YUYUYU, mu kuwa mu yi ta kwankwadar NONON YUYUYU. Sai a hanzarta a tabbatar da cewa ba a yi mana FANCO ballanta mu ce KAICO!