Cincirindon masu kallon Sarkin Zazzau

Dubban Jama’a ne suka taru domin ba wa idanunsu abinci a lokacin da Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya halarci Sallar Juma’arsa ta farko bayan hawa mulki. Jama’ar sarkin sun yi tsinke a ciki da wajen Masallacin Fada inda sarki ya halarci sallar wadda idarwa ke da wuya dubban masoya suka yi turuwa —babu […]

Cincirindon masu kallon Sarkin Zazzau

Dubban Jama’a ne suka taru domin ba wa idanunsu abinci a lokacin da Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya halarci Sallar Juma’arsa ta farko bayan hawa mulki.

Jama’ar sarkin sun yi tsinke a ciki da wajen Masallacin Fada inda sarki ya halarci sallar wadda idarwa ke da wuya dubban masoya suka yi turuwa —babu masaka tsinke— domin kashe kwarkwatar idonsu ta hanyar ganin sarkin.

A ranar Alhamis masu zabar Sarki da kuma gidajen Sarauta na Masarautar Zazzau suka yi mubaya’a ga sarkin.

Zuwa Sallar Juma’ar ita ce fitar Sarkin ta farko tun bayan nada shi a ranar 7 ga Oktoba, 2020.

Ahmed Bamalli shi ne Sarkin Zazzau na 19, wanda kuma ya gaji surukinsa, Sarki Shehu Idris, wanda ya yi mulki na tsawon shekara 45 kafin Allah Ya yi masa rasuwa.

Kafin zamansa Sarki, Ahmed Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma ya fito ne daga gidan Mallawa, daya daga cikin gidaje hudu masu sarautar Zazzau.

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos