Cinikin dan kwallo: Enugu Rangers ta kai karar Raja Casablanca na Maroko

Kulob din Enugu Rangers ya dibar wa kulob din Raja Casablanca na Maroko wa’adin mako biyu a kan cinikin dan kwallonsu Ighodaro Osagouna da kulom din ya sayar wa na Maroko a watan Disambar bara a kan Yuro dubu 150 kwatankwacin Naira Miliyan 37 da dubu 200. A yarjeneniyar da kulob din Enugu Rangers ya […]

Cinikin dan kwallo: Enugu Rangers ta kai karar Raja Casablanca na Maroko
Cinikin dan kwallo: Enugu Rangers ta kai karar Raja Casablanca na Maroko

Kulob din Enugu Rangers ya dibar wa kulob din Raja Casablanca na Maroko wa’adin mako biyu a kan cinikin dan kwallonsu Ighodaro Osagouna da kulom din ya sayar wa na Maroko a watan Disambar bara a kan Yuro dubu 150 kwatankwacin Naira Miliyan 37 da dubu 200.

A yarjeneniyar da kulob din Enugu Rangers ya yi da na Casablanca , sun amince Casablanca za ta biya kudin da ta sayi dan kwallonsu Osagouna ne a kan Yuro dubu 150 sannu a hankali har sau uku amma abin mamaki kawo yanzu kulob din ya kasa biyan na Ranger ko sisin kwabo.
Hakan ta sa Rangers ta yanke shawarar kai kara gaban Hukumar kwallon kafa ta Maroko idan kuma ba a dauki wani mataki ba, to kulob din ya dibar wa na Casablanca wa’adin mako biyu idan ba su cika alkawari ba zai kai kara gaban Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) da kuma ta duniya (FIFA).
Daraktran hulda da ’yan jarida da kuma wayar da kan jama’a na kulob din Enugu Rangers Foster Chime ya ce sun yi mamakin yadda kulob din Maroko bai cika alkawarin da suka kulla tun a watan Disambar bara ba. Ya ce sun amince za a biya su kudin da suka sayar musu da dan kwallonsu Ighodaro Osagouna a kan Yuro dubu 150, kuma za su biya kudin ne sau uku a lokuta daban-daban amma abin mamaki ya zuwa wannan lokaci da nake hira da ’yan jarida kulob din Rangers bai ga ko sisin kwabo daga wajen su ba, al’amarin da ya da suka kai kara gaban Hukumar kwallon kafa ta Maroko.
“Mun rubuta musu wasika sannan mun yi kwafenta ga Hukumar kwallon kafa ta Maroko, sannan mun dibar musu wa’adin makonni biyu muddin ba mu ji daga wurinsu ba, to za mu kai kara gaban Hukumar CAF da ta FIFA don ganin an bi mana kadi.