Cinikin Jariri: Masarautar Kano ta kori Mai Unguwar Fage
Masarautar Kano ta sanar da sallamar Mai Unguwar Sabon Gari, Malam Ya’u Muhammad bisa samun sa da hannu a cinikin wani jaririn da aka tsinta. Sakataren Galadiman Kano Abbas Sunusi, wato Muhammad Umar, shi ne ya sanar da warware rawanin Mai Unguwar a Kano ranar Talata. Kwamandan Hisba da basarake sun sayar da jariri a […]
Masarautar Kano ta sanar da sallamar Mai Unguwar Sabon Gari, Malam Ya’u Muhammad bisa samun sa da hannu a cinikin wani jaririn da aka tsinta.
Sakataren Galadiman Kano Abbas Sunusi, wato Muhammad Umar, shi ne ya sanar da warware rawanin Mai Unguwar a Kano ranar Talata.
- Kwamandan Hisba da basarake sun sayar da jariri a Kano
- An kama limami da basarake da laifin garkuwa da mutane
Ya ce Majalisar Masarautar ta dauki matakin ne bayan wani bincike da Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) ya same shi da hannu a badakalar.
Rahotanni dai sun nuna tun da farko an zargi mai unguwar ne da Kwamandan Hukumar Hizbah na Karamar Hukumar Fagge, Jamilu Yusuf da hannu a ciki.