Cinikin wanda aka ’yanta bayan mutuwa:

Babi na dari da Goma:  Cinikin wanda aka ’yanta bayan mutuwa:672. An karbo daga dan Numair ya ce: “Waki’u ya ba mu labari ya ce, Isma’il ya ba mu labari daga Salmata dan Kuhail daga Adda’u daga Jabir (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya sayar da mudabbari (wanda aka ’yanta bayan […]

Cinikin wanda aka ’yanta bayan mutuwa:
Cinikin wanda aka ’yanta bayan mutuwa:

Babi na dari da Goma: 

Cinikin wanda aka ’yanta bayan mutuwa:
672. An karbo daga dan Numair ya ce: “Waki’u ya ba mu labari ya ce, Isma’il ya ba mu labari daga Salmata dan Kuhail daga Adda’u daga Jabir (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya sayar da mudabbari (wanda aka ’yanta bayan mutuwar shugabansa) saboda wata bukata.”
673. An karbo daga kutaiba ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru ya ce, ya ji Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya sayar da shi (Mudabbari) saboda wata bukata.”
674. An karbo daga Zuhair dan Harb ya ce: “Yakub ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba mu labari, daga Salih ya ce, dan Shihab ya ba da labari cewa: Lallai Ubaidullahi ya ba shi labari cewa, lallai Zaid dan Khalid da Abu Huraira (Allah Ya yarda da su), sun ba shi labari cewa, lallai su sun ji Manzon Allah (SAW) yana tambaya game da wata kuyanga wadda take zina ba ta taba aure ba,” sai ya ce, “Ku yi mata bulalar haddi, sa’an nan idan ta yi zina ku yi mata bulala, sa’an nan idan ta sake zina ta uku, ko ya ce a ta hudu ku sayar da ita.”
675. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Sa’id daga Babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Idan kuyangar (baiwa) dayanku ta yi zina zinarta ta bayyana, to, ya yi mata bulalar haddi, kada ya zarge ta, sa’an nan idan ta yi zina ya yi mata bulalar haddi kada ya zarge ta. Sa’an nan idan ta yi zina ta uku, zinarta ta bayyana to lallai ya sayar da ita, koda da tubkakken igiyar gashi.”

Babi na dari da Goma Sha daya:
Shin mutum zai iya tafiya da baiwa ba tare da sanin ko tana da ciki ba ko a’a? Alhassan bai ganin laifin mutum ya sumbance ta, ko ya rumgume ta.” dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Idan aka yi kyautar baiwa wadda ake saduwa da ita, ko aka sayar da ita, ko aka ’yanta ta, to lallai ta yi tsarkin farjinta bisa tsarkin haila daya babu laifi ga wanda ba a taba saduwa da ita ba. Adda’u ya ce, “Babu laifi mutumin da ya sayi baiwa ya ji dadi da baiwar mai ciki wanda ba nasa ba ban da saduwa da ita.’ Allah Madaukaki Ya ce: “Face matanku ko abin da hannuku na dama ya mallaka” (k:70:30).

676. An karbo daga Abdulgaffar dan Dawud ya ce: “Yakub dan Abdurrahman ya ba mu labari daga Amru dan Abu Amru daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya isa Khaibara, lokacin da Allah Ya ba da nasara a kan manyan masu tsaro. Sai aka ba shi labarin kyan Safiyya ’yar Huyayyi dan Akhdab. Kuma lallai an ka she mijinta lokacin tana an gwanci. Manzon Allah (SAW) ya zabe ta wa kansa, ya fita tare da ita, har sai da muka isa Saddar-Rauha’u lokacin da hailarta ya dauke. Sai (Annabi) ya sadu da ita, sa’an nan aka samar da wani abinci domin walima bisa karamar shimfida. Sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya ce mini: “Yi izini ga jama’ar da ke gefenka, sai haka ta kasance walimar Manzon Allah (SAW) bisa aurensa da Safiyya. Sa’an nan muka fita zuwa Madina, ya ce, “Sai na ga Manzon Allah (SAW) yana lullube ta da alkyabbarsa lokacin tana bayansa. Sa’an nan ya zauna bisa gafen rakuminsa ya bar Safiyya ta dora kafarta bisa gwiwarsa domin ta hau rakumin.”